Yan Bindiga Sun Cinnawa Gidan Sarki Da Mataimakin Kakakin Majalisar Jiha Wuta

Yan Bindiga Sun Cinnawa Gidan Sarki Da Mataimakin Kakakin Majalisar Jiha Wuta

  • Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kona gidajen mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Pascal Agbodike
  • Har wa yau, maharan sun kuma kai hari tare da kona gidan wani basarake a jihar ta Anambra
  • Masu ruwa da tsaki a yankin Anambra South sun yi wani taro na musamman da hukumar zabe INEC don gano hanyoyin magance hare-haren da ke barazana ga zabe

Jihar Anambra - Yan bindiga sun kona gidaje mallakar mataimakin kakakin majalisar jihar Anambra, Pascal Agbodike da wani basarake a jihar Anambra.

Kuma, an kona wasu gine-gine mallakar Osumoghu Nze denis Muomaife kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Taswirar Anambra
Yan Bindiga Sun Cinnawa Gidan Sarki Da Mataimakin Kakakin Majalisar A Najeriya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto cewa yan bindigan na yin barazana ga shugabannin al’ummar da suka zargi da sanadin kawo sojoji garin don su fatattake su daga maboyarsu a cikin dazuzzukan yankin.

Kara karanta wannan

Daga karshe, DSS sun kamo wadanda ke kitsa kone ofisoshin INEC a wata jiha

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi taro da masu ruwa da tsaki na Anambra South da INEC

Sakamakon hakan, masu ruwa da tsaki a Anambra South sun zauna da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, a jihar kan zaben 2023.

An yi taron ne don ilmantar da mutane kan zabe da bita kan batun tsaro a jihar.

Kwamishinan zabe na jihar Anambra, Queen Elizabeth Agwu ta yi tambaya shin ko za a yi zabe a yankin saboda rashin tsaro.

A martaninsa, Osumoghu na Nnewi, Nze Denis Muomaife ya ce wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kona gidajensa.

Ya ce:

"Ba gida na kadai ba, an kona gidan basaraken garin da na mataimakin kakakin majalisar jihar mai wakiltar Ihiala II."

Sai dai, Muomaife ya ce mutanen garin sun kafa kwamitin sulhu don tabbatar da cewa an magance matsalar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

Mahara sun kai mummunan hari a ofishin INEC na jihar Imo

A wani rahoton, a safiyar Litinin 12 ga watan Disamban 2022 mahara sun afka wa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta INEC a Owerri, babban birnin jihar Imo.

The Punch ta rahoto cewa maharan sun lalata ginin ofishin a yayin da suka dasa wani abin fashewa da ake kyautata zaton bam ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164