Wata Kyakkyawar Budurwa ’Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Mutum a Bainar Jama’a, Ta Nuna Tana Kaunarsa

Wata Kyakkyawar Budurwa ’Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Mutum a Bainar Jama’a, Ta Nuna Tana Kaunarsa

  • Wata kyakkyawar budurwa ta ga wani matashi, ta tambayi ya latsa ta ba tare da bata lokaci ba
  • Bidiyon wannan lamari ya ba da mamaki a kafar TikTok, akalla mutane 428k ne suka kalle shi ya zuwa ranar 18 ga watan Disamba
  • ‘Yan TikTok sun bayyana tsoron cewa, akwai yiwuwar mutumin ya yi martani cikin bacin rai ko fada

Wata budurwa a TikTok ta yada wani bidiyon wasan tsokana yayin da ta tunkari wani mutum tare da tambayarsa ya latsa ta.

Bidiyon mai ban dariya da Phoebe ta yada ya zuwa ranar 18 ga watan Disamba, mutum 428k ne suka kalle shi.

A bidiyin, Phoebe ta tunkari mutumin da bata sani ba daga nesa, ta kirashi da babbar murya kan ya biyo ta.

Matashiya ta ce tana son wani, ya watsa mata kasa a ido
Wata Kyakkyawar Budurwa ’Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Mutum a Bainar Jama’a, Ta Nuna Tana Kaunarsa | Hoto: TikTok/@justphoebe_.
Asali: UGC

Yadda ta nemi ya latsa ta

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki

A bidiyon da ta yada, an ga lokacin da take kara shiga jikin mutumin da ya nuna kamar bai san da tana magana ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nuna ba ya sha’awar kula ta, don haka yace babu ruwansa da ita, amma a haka ta ci gaba da yi masa magana.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

A kasa mun tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa bayan ganin bidiyon:

@Victory Roberts:

"Kuma ta haka ta samu soyayya, daga baya suka yi magana, suka rayu cikin farin ciki har abada.”

@Sampizzy:

"Mutumin da abincin rana bai ishe shi bane kike damu. Ke ne wasa ke gabanki.”

@Samson Victor:

"Wasa ya iso ta kaina irin wannan. Kadan ya hana na fasa waya ta.”

@Demiladesmart23:

"Kuma ta haka na hadu mahaifiyarka.”

@faith:

"Wayyo, ina son yarinyar nan.”

Kara karanta wannan

Aiki ja: Hotunan yadda kyakkyawar budurwa ta sauya bayan shiga aikin soja sun girgiza intanet

@_pap.rika:

"Ba kamata ya yi ki latsa ni ba.”

@commentator:

"Mutumin da ya kwana biyu bai ci abinci bane za ki ce ya bi ki.”

Ina Jin Shaukin Soyayya, Ina Son Na Ga ’Ya’ya Na, Amma Na Tsani Aure, Inji Wata Jaruma

A wani labarin, wata jarumar BBNaija ta bayyana yadda ta shirya yin rayuwarta a nan gaba, kuma tana neman saurayin da zai cika mata buri.

Ta kuma bayyana cewa, tana son ta samu 'ya'ya, amma bata da shirin yin aure ko kadan da saurayin da take so.

Hakazalika, ta lissafo wasu sharuddan da take so saurayin ya cika, da kuma abubuwan da za su yi tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.