An Gurfanar Da ’Yan APC da PDP 14 a Jihar Borno Bisa Zargin Hada Tarzoma a Taron Siyasa

An Gurfanar Da ’Yan APC da PDP 14 a Jihar Borno Bisa Zargin Hada Tarzoma a Taron Siyasa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta bayyana kame wasu mutanen da take zargi da tada zaune tsaye a jihar
  • Rundunar ta ce ta gurfanar da wasu mambobin jam’iyyar APC da PDP yayin da suke kokari tada zaman lafiya
  • Ana ci gaba da samun rikice-rikice da maganganu masu tada hankali tsakanin jam’iyyun siyasa da mambobinsu a kasar nan

Maiduguri, jihar Borno - Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa, ta gurfanar da mutum 14 da ake zarginsu da tada husuma a wajen taron gangamin kamfen a jihar.

Wannan na fitowa ne daga bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Maiduguri a ranar Alhamis 22 ga watan Disamba.

Ya bayyana cewa, 12 daga wadanda aka gurfanar din mambobin jam’iyyar PDP ne, yayin da sauran biyu kuma ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP ne, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna: EFCC ta Dira Gidajen Mai, Ta Tirsasa su Rage Farashin Litar Mai

An gurfanar da 'yan APC da PDP a jihar Borno
An Gurfanar Da ’Yan APC da PDP 14 a Jihar Borno Bisa Zargin Hada Tarzoma a Taron Siyasa | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, sauran laifukan da ake tuhumar wadanda mutanen sun hada da tada hakalin jama’a, rashin da’a da kuma jawo raunuka ga wadanda basu ji ba basu gani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manufar 'yan sanda a samu zaman lafiya

Umar ya bayyana cewa, aniyar hukumar ‘yan sanda ne tabbatar da an yi zabe cikin kwanciyar hankali a jihar, inda yace jami’ai za su ci gaba da kama dukkan masu tada hankalin jama’a tare da gurfanar dasu, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa:

“Duk sadda ake yin wani abu na ci gaba, sai an samu wasu da za su zo su bata wannan abu na ci gaba.
“Cewa wai akwai wasu da suke son tarwatsa zaben 2023 wannan ba zai yiwu ba. Ya zuwa yanzu mun kame wadanda ake zargi 119 a wurare daban-daban da ke kokarin tada hankalin jama’a.

Kara karanta wannan

‘Yan Sandan Borno Sun Gurfanar da Mutum 9 Kan Zargin Kaiwa Atiku Hari a Borno

“Allah ya albarka rundunar ‘yan sanda da jami’ai masu yawa. Baya ga ‘yan sandan gama gari da muke dasu, akwai rundunoni hudu na ‘yan sandan mobal da yawansu ya kai 1,8000.
“Wannan wani bangare ne baya ga sauran hukumomin tsaro da aka turo jami’ansu.”

Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su kasance masu sanar da ‘yan sanda motsin dukkan masu son tada zaune tsaye.

An farmaki tawagar Atiku

Idabn baku manta ba, wasu tsageru da ake zargin mambobin APC ne sun farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar a jihar ta Borno.

An farmaki tawagar ne a lokacin da ta kawo gangamin kamfen dinta a jihar da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Ba wannan ne karon farko da ake samun hatsaniyar siyasa tsakanin jam'iyyu ba a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.