Uba Ya Tura Diyarsa Makaranta, Ya Ce Kada Dawo Masa Gida ‘1st Class’
- Wani uba a cikin bidiyo mai ban dariya ya bayyana wasu kalamai masu ban mamaki yayin da ya tura diyarsa jami'a
- Mahaifin ya shaidawa diyarsa cewa, kada ta taba zuwa gidansa har sai ta gama jami'a da sakamako mafi kyau
- A bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, jama'ar da dama sun yi mamaki, sun yiwa diyar fatan alheri da nasara
Wani uba ya ba da mamaki yayin da ya bayyana sharadinsa ga diyarsa da ya tura karatu zuwa wata jami'a.
A wani bidiyon da diyar mai suna @miz_fey ta yada a kafar TikTok, an ga lokacin da mahaifin ke mata gargadin cewa, kada ta yadda ta dawo gidansa sai ta samu sakamako mai kyau na karatu.
Kada ki sa na yi asarar kudi ba
A cewar bidiyon da ta yada, mahaifin ya ce ko dai diyar tasa ta tsaya kan sana'ar hada jakukkuna da jarin N2,000,000 ko kuma ya kashe N20,000,000 ta yi karatun jami'a, amma ta gana da '1st class'.
Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bidiyon ya samu karbuwa a idon jama'ar TikTok, mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali.
Kalli bidiyon:
Martanin jama'a
Precious Joseph:
"Da 20m amma kina maganan ilimin lafiyar kwakwalwa, amma dai wasa kike."
Favieee:
"Ya fi ki je ki yi aure sannan ki bar littafin da 'ya'yanki za su karanta."
A .C.Collection:
"wowwwww, dariya nake kawai kamar yaro ina ma ina da mahaifi kamar wannan."
@godfather:
"Aure ya kamata ki yi ki bar batun littafi."
I_am_Blessing:
"Ku fahimci juna cikin kwanciyar hankali don Allah, kada ki daga masa hankali.”
Onyinye:
“Dole ki dawo da sakamako mai kyau fa ko kuma kawai ki yi aure ya fi don gujewa tattaunawar ahali.”
@elizabethibassey:
“Na gaza daina dariya, iyayen Afrika sun hadu.”
Da shiga aikin soja, budurwa ta sauya kamanni
A wani labarin kuma, wata kyakkyawar budurwa ta shiga aikin soja, bidiyon yadda ta sauya ya ba da mamaki a kafar sada zumunta.
Bidiyo ya nuna lokacin da take zaman gida ba tare da kayan sojoji ba, da kuma bayan kammala horon soja.
Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun bayyana martaninsu mai ban mamaki da kara mata kwarin gwiwa.
Asali: Legit.ng