Tashin Farashin Man Fetur: Jami’an EFCC Sun Dira Gidajen Mai a Kaduna
- Jami’an hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun dinga kai samame gidajen mai a Kaduna
- An tattaro yadda jami’an suka dinga tirsasawa gidajen man siyar da duk lita daya kan N185 a maimakon kusa da N300 da ake siyarwa a kwaryar birnin
- Jami’an sun dinga fatattakar masu siyarn man a jarkoki wadanda suka ce suna boye mai kuma sun tsawwalawa jama’ar gari
Kaduna - Anyi kwarya-kwaryar dirama a fara Laraba yayin da jami’an Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’ammali, EFCC, suka dira gidajen mayuka dake kwaryar birnin Kaduna kan tashin farashin nan fetur.
Da yawa daga cikin gidajen man da jami’an suka kai wa farmaki suna siyar da litar man fetur a sama da 185 da kuma masu siyarwa a jarkoki.
Daily Trust ta tattaro cewa, jami’an EFCC sun dira gidan mai na MRS dake kan titin Akilu dake cikin kwaryar birnin Kaduna wurin karfe 1:30 na rana tare da ‘yan sanda.
Sun zagaya domin tabbatar da cewa gidan man baya siyarwa fiye da farashin da aka gindaya musu yayin da masu motoci ke kan layi don siyan man.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Masu siyar da man sun dakata daga siyarwa yayin da jami’an ke nan amma sun cigaba bayan barinsu wurin.
“Basu boye nan fetur a nan saboda suna siyar da lita kan 185 har da masu siya a jarka, sai dai jami’an EFCC sun fatattaki masu siya a jarka dake farfajiyar.”
- Wani mai mota yace.
Hakazalika, a gidan man Gura Nigeria Limited dake kan titin Nnamdi Azikiwe Bypass, jami’an EFCC din sun dira gidan man inda suka bukaci masu siyarwa su dinga siyar da lita kan N185 ba kan N280 da suke siyarwa ba.
Hakazalika, jami’an sun dira gidan man 5energy dake Mando inda suka dakatar da siyar da man kan 292 duk lita daya.
A Gidan man Usmania kuwa dake Bypass din Nnamdi Azikiwe, an dinga siyar da mai kan 290 amma jami’an EFCC sun umarci a dinga siyar da shi kan farashin da ya dace.
Jami’an sun ziyarci gidan mai na Kamlik Nigeria Limited inda ake siyar da mai kan 299 duk lita daya.
Wani ma’aikacin Hukumar EFCC din da ya bukaci a boye sunansa, yace sun ziyarci gidajen nan ne don su tirsasa su siyarwa kan farashin da gwamnati ta gindaya.
“Abun takaici ne yadda gidajen man basu damu da damuwar ‘yan Najeriya ba. Idan ba haka ba, ta yaya za a siyar da man fetur sama da N185 duk lita daya? Mun da su dole su bi doka.”
- Jami’in yace.
Ba Kaduna kadai nan fetur yayi tashin gwauron zabi ba, har Kano
Legit.ng Hausa ta zanta da wasu masu ababen hawa a kwaryar birnin Kano inda suka tabbatar da cewa sun dinga shan mai har sama da N300 a farkon Disamba.
”A farkon wata Disamba na dinga shan mai a cikin Kano kan N310 a gidan mai na Audu Manager dake kwaryar birnin Kano.
”Daga bisani na fara samun alfarma inda nake fita karfe 6 zuwa 7 na safe domin samun shan mai a kan N184 duk lita a gidan man NNPC.
”Muna fatan Allah ya kawo mana sauki saboda tashin farashin nan fetur yana taba kusan komai a kasar nan.”
- Aliyu Aliyu ya sanar da Legit.ng Hausa.
Asali: Legit.ng