An Kama Matar Dan Majalisa Kan Yunkurin Kasheshi Ta Mallake Dukiyarsa

An Kama Matar Dan Majalisa Kan Yunkurin Kasheshi Ta Mallake Dukiyarsa

  • Wata matar tsohon dan majalissa ta hada baki da wasu tana son gaje dukiyar mijinta tun kafin ya bar duniya.
  • Wanda ta hada bakin da su abokanan mijin nata, daga baya sun so su mallake dukiyar tsohon dan majalissar dan karkatar da ita ko siyarwa
  • Dukiyarsa da ke Uyo da Abuja har ma da babban birnin jihar Rivers wato Port Harcourt suka so su cinye ta.

Abuja: Kotu ta bada umarnin kama Kazia Uwak, tsohuwar matar tsohon dan majalissar wakilai, Robinson Uwak, tare da mika gidan gyaran hali na Suleja da ke Niger.

An gabatar da Joseph Utum da Ibiang a gaban kuliya kan laifin laifin hada hannu da Uwak dan cutar da dan majalissar. Kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku

Laifin da ake zarginsu da aikata wa ya sabawa sashi na 95 bisa ga tsarin bangare na 79 a kasan doka mai lamaba 248 ta koton tarayya.

Mai shari'a M. Inuwa ne ya bada umarnin a tsare wandanda ake zargin a gidan gyaran hali na Suleja, yayin da kuma ya bada umarnin kai saran wato Joseph da abokinsa zuwa gidan gyaran hali na Nasarawa, Keffi.

Kotun Daukaka
Kotu Ta Daure Matar Wani Tsohon Dan Majalisa A Gidan Yari Hoto: The Guardian
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda 'yan sanda suka rawaito sunce wanda ake zargin an kama su ne na kokarin karkatar da dukiyar Uwak zuwa tasu tare da siyar dasu a garuruwan Abuja, Port Harcourt da kuma Uyo.

An dai rawaito cewa matarsa ta dauki wuka ta dabawa mijin nata a kirji a ranar 27 ga watan Mayun wannan shekarar, wanda ya janyo masa rauni mai muni.

Kara karanta wannan

2023: Za Mu Fi Maza Tabuka Abin Azo A Gani, In Ji Yan Takarar Gwamna Mata a Najeriya

A dalilin haka kotu ta ce tana zarginsu da laifi dan haka ta aiki da su gidan yarin kafin ci gaba da shari'ar.

Jaridar Peoples Gazate ta rawaito, cewa da matar ta samu damar caka masa wukar, to da tuni ba wannan labarin ake ba.

Kotu Ta Kori Shugaban Jam'iyya a Nigeria

Wata babbar kotu dake zamanta abuja ta cire shugaban jam'iyyar ADC na kasa Cif Ralph Nwasu, da shugabannin jam'iyyar.

kotun ta fatattaki Nwosu a cikin umarnin da ta bada a ranar Talata 20 ga watan Disamba, yayin sahri'ar da Binta Nyako tayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel