Kaduna: Wutar Lantarki mai Karfi ta Halaka Rayuka 11 a Zaria

Kaduna: Wutar Lantarki mai Karfi ta Halaka Rayuka 11 a Zaria

  • A kalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wata mummunar gobarar wutar lantarki a birnin Zazzau
  • Lamarin ya auku ne sakamakon wutar lantarki mai tsananin karfi da aka kawo a wasu yankunan Gwargwaje da Kauran Juli
  • Hakan yayi sanadiyyar konewar gidan wani Injiniya Zubair Abubakar yayin da wasu gidajen suka tirnike da hayaki

Zaria, Kaduna - A kalla mutane 11 sun rasa rayukansu sanadiyyar wata wutar lantarki mai karfi da aka kawo a wasu yankunan birnin Zazzau dake Zaria a jihar Kaduna.

Taswirar Jihar Kaduna
Kaduna: Wutar Lantarki mai Karfi ta Halaka Rayuka 11 a Zaria. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Gwargwaje da Kauran Juli dake kan babban titin Kaduna zuwa Abuja.

"An kawo wata wutar lantarki mai karfin gaske a yankin ne misalin karfe 1:00 na dare. Hakan ya haifar da tartsatsi ta ko ina a mahadar wutar. Wanda yayi sanadiyyar konewar gidan wani Injiniya Zubair Abubakar yayin da sauran gidajen suka cigaba da fidda hayaki.”

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya Aike Sakon Ta’aziyyarsa ga Iyalan Wadanda Jiragen NAF Sun Halaka Yayin Kashe ‘Yan Ta’adda

- Cewar wani mazauni yankin, Aliyu Samaila.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta tattaro yadda wadanda suka rasa rayukansu suka hada da wata mata mai juna biyu, wata jami'ar kiwon lafiya, wani 'dan sanda da sauran wasu da dama a yankin Gwargwaje.

Mrs Christy Lombo, matar 'dan sandan da ya rasa ransa sanadiyyar gobarar lantarkin a barikin 'yan sanda na Gwargwaje, ta bayyana yadda suke bacci lokacin da aka kawo wutar.

"'Diyata ta tashi da dare, inda ta ga hayaki a wasu wurare a gidan. Hakan yasa ta tashe ni, sai dai kafin nan mijina ya riga ya tashi tare don ya kashe mahadar wutar gaba daya gidan.
"Take yanke shokin ya kama shi gami da bugar dashi kasa saboda karfin wutar. Daga bisani muka garzaya dashi asibiti inda ya ce ga garinku.”

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Dakaru Sun Sheke Hatsabibin Ɗan Bindiga da Yaransa 12 da Suka Addabi Jihohin Arewa 4

- A cewarta.

Kakakin hukumar wutar lantarki na Kaduna (KEDCO), Abdulazeez Abdullahi, a wata takarda da ya fitar ya ce binciken da aka yi ya bayyana cewa:

"Lamarin ya auku ne sakamakon wuta mai karfi da aka kawo ta waya mara karfi, wacce tayi sanadin sakin wuta ba bisa ka'ida ba.
"An hanzarta bude hanyar shanye wutar cikin gaggawa don gudun cigaba da barna.
"Mun cigaba da lura da lamarin, sannan mun sanar da aukuwar mummunan lamari. Muna bayyana alhininmu da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu bisa aukuwar lamarin."

Haka zalika, KEDCO ta jinjinawa Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, bisa gudunmawar da ya bada bayan aukuwar lamarin.

A zantawa da Legit.ng tayi da wata ‘yar uwar mai juna biyun da ta rasa ranta a Kauran Juli, ta sanar da cewa wuta ce aka kawo mai karfi wacce tayi musu tartsatsi da fashe-fashe.

Ta sanar da cewa cikin dare aka kawo ta kuma tayi yunkurin kashe Kayayyakin wutan da suka fara kamawa ne inda wutar ta kama ta tare da make ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng