Ana Kukan Bashi Ya Yi Katutu, Buhari Yana Kokarin Sake Karbo Aron N0.8tr
- Shugaba Muhammadu Buhari ya rubutawa ‘yan majalisa wasika domin ba shi damar cin wani bashi
- Duk da ana bin Najeriya bashin kudi masu yawa, gwamnatin tarayya tana neman aron wasu N819bn
- Za a karbo sabon bashin ne saboda ambaliyar ruwan sama da ya yi barna a wasu jihohi a shekarar nan
Abuja - Bashin da ake bin Najeriya a gida ya tashi zuwa N22.57tn a yayin da gwamnatin tarayya ta gabatar da wani karin kasafin kudi na shekarar 2022.
A makon nan ne shugaba Muhammadu Buhari ya aikawa ‘yan majalisa takarda, yana so su amince da sabon kundin kasafin kudin kusan Naira Biliyan 900.
Punch ta ce za a nemo kudin da za a aiwatar da kasafin kudin nan ne ta hanyar cin bashi a cikin gida. Hakan zai kara adadin bashin da kasar za ta biya nan gaba.
Idan majalisar tarayya ta amince da bukatar shugaban Najeriyan, za a karbo bashi domin a sake gina abubuwan more rayuwa da aka rasa a dalilin ambaliya.
Majalisa na da wuka da nama
Kwamitocin kasafin kudi, ayyuka, tattalin arziki da wasunsu za su zauna a majalisar dattawa domin su duba cancantar daga adadin tulin bashin da ake bin kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A shekarar nan, ambaliyar ruwan sama ya yi illa a jihohi da-dama. Daga cikin inda abin ya fi yin tasiri akwai Jigawa, Bayelsa da Kano, an rasa dinbin dukiya.
Bashin da za a karba a 2022 zai karu
Rahoton ya nuna cewa da farko gwamnatin tarayya tayi niyyar cin bashin N5.01tn ne a shekarar nan domin cike gibin N6.26tn da ke cikin kasafin kudi.
Daga cikin bashin da za a ci a bana, za a karbo N2.51tn daga hannun bankunan da ke gida.
A dalilin canjin da aka samu yanzu na kara karbo aron N819.54bn, bashin da ake bin gwamnatin Najeriya zai karu zuwa N3.33tr kafin shekara mai zuwa.
Yadda tulin bashi yake tashi
Bayanan da aka samu daga ofishin DMO mai kula da bashin gwamnatin tarayya, ya nuna har karshen Disamban 2021, ana bin Najeriya bashin N19.24tn ne.
Zuwa Satumban shekarar nan ta 2022, sai da bashin ya karu zuwa N21.55tn. Ma’anar hakan kuwa shi ne gwamnatin Buhari ta ci bashin N2.31 a shekarar bana.
A tsarin da aka yi, gwamnatin kasar tana da damar kara karbo aron N1.02tr a gida. Bisa dukkan alamu tun da shekarar ta zo karshe, a N819bn za a tsaya.
Gwamnati ta samu N300m
An samu rahoto Lauyoyin hukumar EFCC sun fara yin galaba a shari'arsu da tsohon Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris a kan zarginsa da taba baitul-mali.
Baya ga kudi masu yawan gaske, kotu ta ce Gwamnati ta karbe Kano City Mall/Al Ikhlas Shopping Mall da wasu gidajen tsohon AGF din a Kano da Abuja.
Asali: Legit.ng