Ina Jin Shaukin Soyayya, Ina Son Na Ga ’Ya’ya Na, Amma Na Tsani Aure, Inji Wata Jaruma
- Jarumar wasan sharholiya na BB Naija ta bayyana irin rayuwar da take son kullawa da duk wanda ya yi sa'an samunta
- Ta ce tana kaunar rayuwar jin dadi da sharholiya, amma bata kaunar ta yi aure, duk da kuwa tana son 'ya'ya
- Ta yi tsokaci game da abubuwan da ta shirya yi idan ta samu irin namijin da za ta yi rayuwa dashi a gaba
Najeriya - Daya daga cikin tsoffin jaruman BB Naija, Tega Dominic ta bayyana cewa, tana kaunar samun abokin rayuwa, amma ba ta son batun aure.
Jarumar ta wasannin sharholiya ta bayyana hakan ne a wani rubutun da ta yi a Twitter, inda ta bayyana irin saurayi ko abokin rayuwa da take son samu.
Ta bayyana cewa, tana kaunar wanda za ta yi komai tare dashi, ciki har da samu 'ya'ya, su hada asusun banki guda daya da dai sauran abubuwan gaske na rayuwa.
A kalamanta:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina son abokin rayuwa mai kamun kai, kwarin gwiwa, matukar kaunata, tausayi, abokin harka, za mu iya tara 'ya'ya, mu rayu tare, mu more rayuwar juna tare, mu gina rayuwa tare, mu ma tara kudi a asusu daya, amma banda aure."
A shirye nake idan da mai bukata, ina kan baka ta
A wani rubutun da ta sake yi a kafar ta Twitter, Dominic ta kara da cewa, a shirye take ta fara kulla alaka idan ta samu irin wannan namiji da za su yi sharholiyar rayuwarsu tare.
Ta kuma yi rantsuwar cika dukkan abin da ta bayyana matukar hakan zai ba su biyun farin ciki da annashuwa a rayuwar da za su yi.
Ta bayyana cewa:
"Abin dariya kalli abinci!! Hakan ya nuna abin da mutane ke so kuma har ma da kaskantattu, kafar yanar gizo na son tada kura, abin al'ajabi!!
"Amma fa zan samu abin da nake idan ina son hakan, matukar hakan zai ba abokin rayuwata farin ciki kuma mu rayu rayuwa mai nisa sabanin irin taku munafukai."
Ba wannan karon ne na farko da ake samun jaruman fina-finai ko na wasannin kwaikwayo na bayyana ra'ayinsu na kin aure ba.
Wani matashi kuma ya bayyana irin matar da yake nema zai aura, ya bayyana ka'idoji da sharrudan da za ta cika.
Asali: Legit.ng