'Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Motocin Sintirin Yan Sanda a Kogi

'Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Motocin Sintirin Yan Sanda a Kogi

  • 'Yan bindiga sun kashe jami'an hukumar yan sandan Najeriya guda biyu a jihar Kogi ranar Laraba 21 ga watan Disamba 2022
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kogi, William Aya, yace lamarin ya faru ne a kan Titin Agbaja, Lokoja
  • Tuni dai kwamishinan yan sanda ya ƙara tura dakaru na musamman amma kafin isarsu maharan suka tsere

Kogi - Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta rasa biyu daga cikin jami'anta yayin da wasu 'yan bindiga suka farmaki tawagar dakarun Sintiri ranar Laraba, 21 ga watan Disamba, 2022.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, William Aya, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Jami'an yan sanda.
'Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Motocin Sintirin Yan Sanda a Kogi Hoto: punchng
Asali: UGC

Ya ce lamarin ya auku ne a kan Titin Agbaja, Lokoja babban birnin jihar Kogi sa'ilin da maharan suka fito daga ciki Jeji suka farmaki tawagar dakarun bayan sun isa wurin kamar yadda suka saba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya Aike Sakon Ta’aziyyarsa ga Iyalan Wadanda Jiragen NAF Sun Halaka Yayin Kashe ‘Yan Ta’adda

Aya ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A halin yanzun hukumar 'yan sanda ta rasa dakarunta guda biyu yayin artabun musayar wuta da wasu tsageru, sun tsere tun kafin isowar ƙarin jami'ai da aƙa tura kai ɗauki."

Wane mataki aka ɗauka bayan faruwar haka?

Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa tuni kwamishina ya umarci a kara tura dakaru na musamman domin zakulo miyagun duk inda suka shiga.

A ruwayar Daily Trust, ya kara da cewa:

"Nan take kwamishinan 'yan sanda na jihar Kogi, CP Akeem A. Yusuf, ya tura ƙarin jami'ai na musamman zuwa yankin domin su bazama nemo maharan su cafko su kana a gurfanar da su."
"Haka nan kwamishinan ya umarci mataimakinsa na sashin bincike da ya hanzarta fara bincike kan lamarin."
"Ya kuma yi kira ga ɗaukacin al'umma da ke zaune a yankin su taimaka wa jami'ai da sahihin bayanai kan miyagun domin su shawo kan lamarin tun da wuri."

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram Sun Kai Hari, Sun Kone Gidaje 7, Kayan Abinci da Dabbobin Jama’a

A wani labarin kuma Gwamna Matawalle Ya Faɗi Gaskiyar Abinda Ya Faru Har Jirgin Soji Ya Kashe Mutane a Zamfara

Gwamna Bello Matawalle ya tabbatar da samun akasi yayin da jirgin yakin sojin Najeriya yake wa yan ta'adda luguden wuta a Malele da Mutunji, ƙaramar hukumar Maru.

Gwamnan ya jajantawa mutanen da abun shafa kuma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa zata agaza masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262