Jarirai 200 Aka Haifa A Sansanin Yan Gudun Hijira A Jihar Benue

Jarirai 200 Aka Haifa A Sansanin Yan Gudun Hijira A Jihar Benue

  • Jarirai kusan dari biyu aka haifa a jihar Benue aka haifa a sansanin yan gudun hijra a babban birnin jhar Makurdi
  • An haifi jariran a cikin matsin rashin ishashen magani da kuma wasu bukatu da ake bukatar mai haihuwa ta samu
  • Sakataren NEMA, ne ya sanar da hakan a lokacin da yake bayanin aiyukan hukumar a daya daga cikin sansanin a Makurdi

Benue: Babban sakataren hukumar kula da hukumar kai agajin gaggawa da tallafi NEMA, Dr Emmanuel Shior yace an samu mata da suka haifi jariari kusan 200 a sansanin yan gudun hijira da ke Makurdi.

"Muna da jarirai sama da 200 da muka san an haifesu a nan."

Sakataren yace "wadannan jariran da aka haifa ba'a shigar dasu kundin shigar da bayanai na jarirai ba. Akwai kuma wasu wanda su kuma an haifesu kuma mun shigar da su cikin rijistarmu."

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

Jarirai
Jarirai 200 Aka Haifa A Sansanin Yan Gudun Hijira A Jihar Benue Hoto: Peoples Gazzate
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace akwai kimanin masu gudun hijira kusan mutum miliyan biyu da suke zaune a sansanonin yan gudun hijira a gfadin jihar. kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Yace mun shigar da bayanan da yawa da cikin yan gudun hijiran da suka riga mu gidan gaskiya. wasu sun rasu ne dalilin rashin lafiya, wasu annoba wasu kuma daga kokarin gujewa masu kai mjusu hari.

Yanayin Sansanin Yan Gudun Hijira

Peoples Gazzate ta rawaito sakataren na cewa ina mai nadamar sanar muku da cewa jami'an tsaron jihar Benue basa wani yunkuri na ganin sun tseratar ko tsare yadda yan gudun hijira ke rayuwa.

Sakataren yace hukumar ta raba kimanin buhuhunan shikafa guda 4,000 zuwa 5,000 da taliyar yara, da dai sauran abubuwan bukatun yau da kullun ga yan gudun hijirar.

Kara karanta wannan

Rikici Kan Bazawarar Yan Bindiga Ya Janyowa Mutane Asarar Rayukan Mutum 69 a Zanfara

Yan Gudun Hijira A Barno Sun Haifi Jarirai Sama Da 3000

Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta duniya tace an haifi jariari 17,053 a sansanonin 'yan gudun hijira na jihar Barno a cikin shekaru uku, kamar yadda wani rahotan BBC Hausa ya nuna.

Kwamitin majalissar dinkin duniya mai kula da yan gudun hijara, ya fadawa kamfanin dillacin labarai na Nigeria cewa an haifi yaran ne a sansani 18 da ke jihar.

Mista Frantz Celestin shi ne shugaban kwwamitin ya ce sun hada gwuiwa da hukumar kidaya ta Nigeria da kuma asusun kula da kanannan yara na majalissar Dinkin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel