Kano: Rashin Zuwa Shaida Ya Kawo Tsaiko a Shari'ar Kisan Ummita
- Bangaren gwamnati masu shigar kara ya kawo tsaiko a zaman ci gaba da shari'ar Ɗan China wanda ya kashe Ummita a Kano
- A karo na biyu a jere, shaidar masu kara watau gwamnatin Kano na karshe bai samu halartar zaman Kotun ba a jiya Talata
- Alkalin Kotun ya amince da bukatar lauyan gwamnati na ɗage zaman zuwa washe gari ranar Laraba 21 ga watan Disamba
Kano - An samu tsaiko a Shari'ar ɗan China mazaunin Kano, Geng Quanrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyarsa, Ummukulsum Sani Buhari, sakamakon rashin zuwan shaidan masu ƙara.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa rashin zuwan shaidan ya jawo tsaiko a ci gaba da sauraron shari'ar a gaban babbar Kotun Kano karkashin jagorancin Mai shari'a Sanusi Ado Ma’aji kwana biyu kenan a jere.
Idan baku manta ba a zaman karshe, Mai shari'a Ma'aji ya ɗage zaman zuwa ranakun 19, 20 da 21 ga watan Disamba domin dawowa a saurari shaidar masu shigar na ƙara da karshe.
Yayin da aka dawo zaman ranar Talata, Lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari'a, M.A Lawan, ta bakin hadiminsa, Wada A. Wada ya faɗa wa Kotu cewa shaidan na da mara lafiya a Asibiti da za'a yi wa aiki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wada ya nemi afuwar kotu da kuma Lauyan wanda ake tuhuma bisa gazawarsu wajen gabatar da shaida ta karshe kana ya nemi mai shari'a ya ƙara masu lokaci.
"Cikin nadama muna mai ba da hakurin rashin zuwan shaidar mu na karshe yau, mahaifinsa ne ke kwance ba lafiya kuma shi ne ke zaune a wurinsa shiyasa bai samu damar zuwa ba."
"Sakamakon haka muna baiwa Kotu da ɓangaren masu kare wanda ake ƙara hakuri."
- Wada A. Wada.
Barista Wada ya roki Kotu ta taimaka ta ɗaga zaman zuwa washe gari ranar Laraba (Yau) inda ya tabbatar da cewa shaidan zai samu zuwa insha Allahu.
A nasa ɓangaren lauyan dake kare ɗan China, Barista Muhammad Balarabe Dan’azumi, bai yi ja in ja kan zancen ɓangaren gwamnati ba.
Daga nan sai Alkalin Kotun ya ɗage zaman zuwa ranar Laraba 21 ga watan Disamba, 2022 domin ci gaba da sauraron shaidu, kamar yadda Aminiya ta rahoto.
Wata Matsala Ta Kunno Kai a Zaman Shari'ar Dan China Wanda Ya Kashe Ummita a Kano
A wani labarin kuma kun ji cewa a zama Baya Kotu ta ɗage zaman shari'ar saboda wanda ake ƙara ba shi da lauya mai tsaya masa
Saboda girman laifin da ake tuhumarsa a kai, alkalin ya amsa rokon Mista Geng na neman a bashi dage shari'a don ya kira lauyansa da zai kare shi.
Asali: Legit.ng