Wata Matsala Ta Kunno Kai a Zaman Shari'ar Dan China Wanda Ya Kashe Ummita a Kano

Wata Matsala Ta Kunno Kai a Zaman Shari'ar Dan China Wanda Ya Kashe Ummita a Kano

  • Babbar kotun jihar Kano ta dage sauraron shari'ar dan China, Geng Quangrong, wanda ake zargi da kashe budurwarsa yar Kano
  • Justis Sanusi Ado Ma’aji ya dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba saboda rashin lauya da zai kare wanda ake tuhuma
  • Saboda girman laifin da ake tuhumarsa a kai, alkalin ya amsa rokon Mista Geng na neman a bashi dage shari'a don ya kira lauyansa da zai kare shi

Kano - Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Justis Sanusi Ado Ma’aji ta dage sauraron karar dan kasar China, Geng Quangrong, wanda ake zargi da kashe masoyiyarsa yar Najeriya, Ummukulsum Sani Buhari.

Daily Trust ta rahoto cewa an dage zaman ne saboda rashin zuwan lauyan da zai kare wanda ake zargin.

Dan China da budurwa
Wata Matsala Ta Kunno Kai a Zaman Shari'ar Dan China Wanda Ya Kashe Ummita a Kano Hoto Daily Trust
Asali: Twitter

A yayin zaman na ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, Quarong, ya roki kotu da ta dage zaman domin bashi damar kiran lauyansa da zai tsaya masa.

Kara karanta wannan

2023: Peter Obi da Magoya-bayansa Sun Ci Karo da Cikas Ranar da Aka Fara Kamfe

Da yake martani, Atoni Janar na jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan bai nuna adawa da rokon wanda ake kara ba na neman a dage shari’ar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Lallai wannan shari’ar ba zai ci gaba ba a yau ba tare da lauya da ke kare wanda ake zargi ba. Laifin da ake tuhumarsa a kai babban lamari ne. A cikin wannan hali, muna neman a dan dage sauraron karar don baiwa wanda ake zargi damar samun lauya.”

Justis Ma’aji ya dage sauraron shari’ar zuwa 4 ga watan Oktoba, rahoton Aminiya.

Ana dai zargin Mista Geng da kashe Ummitah, matashiya mai shekaru 23.

Marigayiyar da wanda ake zargin suna soyayya da junansu kafin alakarsu tayi tsami.

Kisan Ummita: An Gurfanar da ‘Dan Chana, Kotu ta Yanke Hukuncin Farko

A baya mun ji cewa, wata kotun Majistare da ke zama a kotu ta yi umurnin garkame ‘dan kasar China, Geng Quanrong, kan kisan masoyiyarsa yar Najeriya, Ummukulsum Sani Buhari.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta tasa keyar wani sarkin gargajiya zuwa gidan yari saboda laifuka biyu

Kotun ta yi umurnin tsare wanda ake zargin a gidan gyara hali na Kurmawa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Umurnin kotun ya biyo bayan gurfanar da wanda ake zargin da yan sanda suka yi a gaban kotun kan tuhumar aikata kisan kai wanda yayi karo da sashi na 221 na Kundin Pinal Kod.

Asali: Legit.ng

Online view pixel