Shugaba Buhari Ya Bukaci Majalisar Tarayya Ta Hanzarta Amincewa da Karin Kasafi
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar wakilan tarayya da ta amince da karin naira biliyan N89.5bn a kasafin 2022
- Buhari ya kuma tura da wannan bukata ga majalisar dattawa, inda ya ce gwamnatinsa zata kara ciyo bashi don aiwatar da kasafin
- A cewar shugaban kasan za'a yi amfani da karin kuɗin wurin karisa manyan ayyuka duba da yadda Ambaliya ta yi ɓarna a sassan kasa
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar tarayya ta hanzarta amincewa da karin kasafin kuɗi na Biliyan N819Bn, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ne ya karanta sakon bukatar shugaban kasan yayin zamansu na yau Laraba, 21 ga watan Disamba, 2022.
Buhari yace ƙarin kan kasafin kuɗin shekarar 2022 za'a yi amfani da shi ne samar da kuɗin ci gaba da muhimman ayyukan raya ƙasa a dukkanin sassan ƙasar nan.
Shugaban ya ƙara da cewa ibtila'in Amaliyar ruwan da aka sha fama da ita a damunar 2022 ta lalata wasu muhimman ayyukan gwamnati a ƙasar nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Buhari ya tura wa majalisar dattawa karin kasafin
Haka zalika, shugaban kasan ya nemi Sanatoci su amince da karin kasafin na N819.5bn a cikin wata wasika da ya aike wa Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa kuma ya karanta a zauren ranar Laraba.
Buhari yace gwamnatinsa zata samar da kuɗin ƙarin kasafin ta hanyar ciyo bashi kuma za'a yi amfani da su wurin ƙarisa kammala ayyuka waɗanda Ambaliya ta taɓa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya faɗa wa Sanatocin cewa Ambaliyar ruwan da aka sha fama da ita a 2022, ta lalata hanyoyi a mafi yawan sassan ƙasar nan. Ƙarin kasasfin zai taimaka wurin gyara su inji shi.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da Femi Gabajabiamila sun tattauna kan batun sabon tsarin da babban bankin Najeriya CBN ya bullo da shi.
Yayin ganawarsu, kakain majalisar wakilan tarayya yace sun kuma taba batutuwan da suka shafi babban zaɓen 2023 da ke tafe.
Asali: Legit.ng