Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Yadda Ta Sauya Kamanni Sun Bada Mamaki

Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Yadda Ta Sauya Kamanni Sun Bada Mamaki

  • Wata kyakkyawar budurwa da aka yada hotunanta kafin da bayan ta shiga aikin soja ta ja hankalin jama’a
  • An ga fuskarta ta matukar sauyawa ba tare da kwalliya ba yayin da take sanye da kakin soja, ga kuma ta yi aski
  • Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi martani kan wannan jami’ar soja, sun ce aikin soja ba na rago bane

Wata kyakkyawar budurwa, @ohemaarosepapabi ta bayyana a kafar sada zumunta don nunawa duniya hotunanta da yadda ta sauya bayan shiga aikin soja.

Da take yada hotunan, ta nemi mutane su duba su ga yadda ta sauya bayan da ta kammala horon zama soja.

A farkon bidiyon da ta yada, gata nan cikakkiyar mace, diri da surarta gaba daya sun bayyana a matsayinta na mace. Dakiku kadan gaba, fuskarta ta sauya, da wuya ma a iya gane ta.

Kara karanta wannan

Aiki ya jika: Bayan kowa ya yi ankon N150k, amarya ta fece, ango da abokansa sun girgiza

Bidiyo da hoton sauyawar wata budurwa sun ba da mamaki
Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Yadda Ta Sauya Kamanni Sun Bada Mamaki | Hoto: TikTok/@ohemaarosepapabi
Asali: UGC

Karshen bidiyon ya nuna lokacin da take sanye da kayan sojoji ne, babu gashi mai yawa a kanta, ga kuma fuskarta babu maikon ado.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A gefenta kuwa, an ga wani jami’in soja da ke tsaye. A takaice dai, hotunan sun nuna ta sauya karara bayan shiga aikin soja.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, akalla murane 200 ne suka yi martani, mutum sama 14,000 sun yiwa bidiyon dangwalen nuna sha’awa.

Ga kadan daga martanin jama’a:

Brymo:

"Yanzu dai kinyi kama da mutumin da kika dauki hoton nan dashi.”

Linda korang:

"Aikin nan dole ya nutsar dake.”

emmanuelnanakojom:

"Kada ki damu, kyawunki zai dawo.”

adwoakordie13:

"Zan fito kamar tsutsa, dukkan kasusuwane a karye, duk da haka na taya ki murna.”

Brownexia:

"Duk da haka kina da kyau. Kawai dai kin kara karfi ne.”

Kara karanta wannan

Kamar da wasa: Amarua ta ce ba za a daga bikinta ba, ta zo wurin biki da ciwo a kafa

lawrenceacheampo35:

"Babban sauyi.”

pEArl:

"’Yan mata kin sauya sosai ina bukatar hotonki na soja don tuna wacece ke. Wow tsawon lokaci ban ganki ba.”

Duk da rauni a kafa, amarya ta ace ba mai daga aurenta

Wata amarya ta ba da mamaki yayin da ta bayyana a lokacin daura aurenta duk kuwa da raunin da take dashi.

A wani bidiyo, amaryar ta ce tana da raunin da aka yi mata tiyata wata guda kafin auren, amma a haka ta amince a daura.

Jama'ar kafar sada zumunta sun bayyana ra'ayinsu da ganin wannan bidiyon, mun tattaro muku martanin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.