Matawalle Ya Tabbatar da Kashe Mutane da Dama Yayin Luguden Jirgin Soji a Zamfara
- Gwamnan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya ya yi jawabi ga mutanensa kan akasin da jirgin soji ya samu a kauyuka 2
- Gwamnan wanda ya tabbatar da rasa fararen hula da dama a lamarin, yace gwamnati zata tallafa wa iyalan mutanen
- An tattaro cewa akalla fararen hula 68 suka mutu da Sojoji amma an kashe 'yan ta'adda sama da 200 a samamen
Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya tabbatar da cewa fararen hula da dama da Sojoji ne suka rasa rayukansu yayin luguden sojin sama a ƙauyukan Malale da Mutunji, karamar hukumar Maru ta jihar.
Channels tv ta rahoto cewa Gwamnan bai bayyana adadin mutanen da basu ji ba kuma ba su gani ba suka rasa rayuwarsu sakamakon lamarin.
Ganau sun bayyana cewa fararen hula 68 suka mutu sakamakon samamen jirgin sojin yayin da wasu 40 suka jikkata. Amma kwamandan dakarun Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Uwem Bassey yace ba wani abu kamar haka.
Zamfara: Matawalle ya Aike Sakon Ta’aziyyarsa ga Iyalan Wadanda Jiragen NAF Sun Halaka Yayin Kashe ‘Yan Ta’adda
Sai dai a wani jawabin kai tsaye, gwamna Matawalle ya yi bayanin cewa dakarun tsaro na aikin kakkaɓe 'yan ta'adda waɗanda suka hana mazauna zaman lafiya Malele da Mutunji lokacin da aka samu akasin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane mataki gwamnatin Zamfara ta ɗauka?
Gwamna Matawalle ya yi amfani da wannan dama ya miƙa sakon jaje da ta'aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa da na Sojojin da suka rasa rasu suna tsaka da bauta wa ƙasa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Zamfara zata tallafa wa iyalan waɗanda suka mutu sanadin matsalar da aka samu.
Matawalle ya jaddada kudirim gwamnatinsa na taimaka wa hukumomin tsaro da kayan aikin da suke bukata a yaƙin da suke da masu aikata ta'addanci waɗan da suka hana Zamfarawa bacci da ido biyu.
Yadda Jirgin ya yi ajalin mutane a Zamfara
"Ban Sani Ba Sai Daga Baya" Gwamnan Arewa Ya Umarci a Hanzarta Sakin Wanda Ya 'Zage' Shi a Soshiyal Midiya
A wani labarin kun ji cewa mutane da dama sun rasu sakamakon samamen jirgin yakin sojin Najeriya a jihar Zamfara
Mazauna garin su shida cewa sama da mutane 60 da suka ƙunshi mata da kananan yara ne suka mutu amma 'yan ta'adda aka fi kashewa a harin.
Wasu bayanai da aka tattara bayan lamarin sun nuna cewa samamen sojin sama ya halaka 'yan bindiga sama da 200.
Asali: Legit.ng