Atiku Ko Obin Wa, Baza Su Iya Ba, Nine Wanda Na Fi Kowa Cancanta
- Dole martani tsakanin 'yan siyasa yai zafi, ana shiga watan farko na shekarar 2023 za'a iya cewa komai yadau dumi domin a watan biyu za'a kada kuri'a
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, yace shi kadai zai, iya, shine shago a tsakanin yan takarar nan
- Atiku da Obi makaryatane, ba su da gaskiya baza su iya mulkin Nigeria ba, nine kawai zan iya.
Abuja: Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu yace a ranar talatan nan, shi shago ne, kuma mai gaskiya yana mai cewa sauran yan takarar basu da gaskiya.
Tinubu na magana ne a taron masu ruwa da tsaki da yan jam'iyyar suka shirya masa a Calabar babban birnin jihar Cross River. Kamar yadda PMNewsNigeria ta hakkaito.
"Burina da manufa, itace ciyar da kasar nan gaba, bani da wani buri da wuce haka, wanda duk sauran yan takarar basu da shi"
Tinubu yace:
"Duk wanda suke takarar nan basu da gaskiya, kai basu da alamar gaskiya ma atattare da su, karye suke fada, shi yasa kullum basu da wata magana illa zagi na"
Tinubu bai gushe ba yana magana sai ya tabo batun ya ingancin a takarar nan take, Tinubu yace
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ni shago ne, bani da abokin dambe, ni kawai Nigeria ce a gaba na"
Tinubu yace in aka zabe shi zai magance matsalar talauci da tai wa kasar nan katutu, kuma zai yi duk mai yiwa wajen tabbatar da abubuwan da sukaa kamata na abinda yan kasa ke bukata. Tinjubu yace Ilimi shine abinda zai yaki talauci, yace zasu tabbatar an samu mai inganci.
Kan batun hadin kan kasa kuwa Bolan, yace ya na mai tabbatarwa da 'yan Nigeria zai hade kansu tsaf, baza a samu wata baraka ko sabani a tsakanin yan kasa ba.
Dan takarar shugaban kasa na wannan jawaban ne a jihar Cross Rivers, inda ya bayyana jihar a matsayin wata cibiyar yawan bude ido a nahiyar Africa.
Peoples Gazate ta rawaito cewa tunda fari gwamnan jihar Cross-River Ben Ayade yace akwwai bukatar kasan nan ta koma ta farkin noma indai ana so a yaki yunwa a tsakanin yan kasa
Ayade yace yadda kasar nan ke da filayen noma amma an watsar da su ba'a amfanarsu, kamar yadda ya kamata.
"Abin kunya ne a garemu kamar yadda muke da cocoa amma muna da talauci, bamu da kamafanin da zai sarrafashi"
Ayi Tunubu Da Alheri Inji Gwamnan Jihar Rivers
Gwamnan jihar Rivers yace yayi mun gani a jihar Lagos, da yadda ya sarrafa tekun Atlantic ya zama hanyar samun kudin shiga.
Ina mai tabbatar muku kuka zabeshi zai yiwa Nigeria abinda ya fi wannan muddin dama da yake so kun bashi.
Asali: Legit.ng