Bayanai Sun Nuna ’Yan Najeriya Sun Fi Son Hada-Hadar da Ba Ta Tsabar Kudi Ba, Sun Kashe Sama da N345trn

Bayanai Sun Nuna ’Yan Najeriya Sun Fi Son Hada-Hadar da Ba Ta Tsabar Kudi Ba, Sun Kashe Sama da N345trn

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) na ci gaba da duba hanyoyin habaka amfani da kudaden zamani sabanin takardun da aka saba dasu
  • Sabon kudurin bankin CBN na rage yaduwar kudade a hannun jama’a zai fara aiki ne a watan Janairun 2023, zai kuma ba da damammaki da yawa
  • Bayanai da aka samo daga cibiyar NIBSS sun nuna cewa, a cikin watanni 11 na 2022, ‘yan Najeriya sun yi hada-hadar kudade N345.04tr

Najeriya - Daga ranar 9 ga watan Janairun 2023, Babban Bankin Najeriya (CBN) zai tabbatar da dokarsa a kan injunan ATM, POS da sauran hanyoyin cire kudi a kasar nan.

Manufar CBN ba komai bane face rage adadin kudaden da ke yaduwa a hannun jama’a tare da daura ‘yan kasar a turbar amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani.

Kara karanta wannan

Labari mai kayatarwa: Ahmad Musa ya gina katafariyar cibiyar wasanni a wata jihar Arewa

Babban bankin na son ganin ‘yan Najeriya na amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani ta yanar gizo ko sabanin haka a madadin tsabar kudi jingim a hannu.

Kudin da 'yan Najeriya suka kashe a 2022
Bayanai Sun Nuna ’Yan Najeriya Sun Fi Son Hada-Hadar da Ba Ta Tsabar Kudi Ba, Sun Kashe Sama da N345trn | Hoto: NIBSS
Asali: Facebook

Hanyoyin da ake son amfani dasu sun hada da yanar gizo, USSD, POS, manhajojin waya, ATM da dai saransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda ‘yan Najeriya suka yi amfani da sabbin hanyoyin biyan kudi a 2022

Bayanan da aka samo daga cibiyar hadakar bankuna ta NIBSS sun nuna cewa, ‘yan Najeriya sun yi amfani da hanyoyin zamani wajen kashe kudaden da suka kai tiriliyan 345.04 a watanni 11 na 2022.

NIBSS ce ta kula da dukkan hada-hadar da aka yi ta hanyar biyan nan take (NIP) da suka da; biya ta intanet, wayan hannu, ATM, POS da USSD.

Tsarin NIP dai wani tsari ne da ake amfani dashi wajen biyan kudi nan take ga lambar asusun banki, an fara amfani da NIP a 2011, NIBSS ce ta samar dashi.

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: 'Yan sanda sun kama wasu tsagerun masu garkuwa da mutane

Adadin kudaden da aka yi hada-hada ta yanar gizo

  • POS- N7.56trn
  • Wayoyin hannu- N16.9trn

Adadin kudaden da aka yi hada-hada ta wasu hanyoyin zamani

  • POS - N1.06bn
  • Wayoyin hannu - N609.4bn
  • Takardun ceki -3.72m
  • Tsarin NIP - 4.57bn
  • Biya ta yanar gizo - 8.4m

Idan baku manta ba, na daga tsarin CBN kirkirar sabon kudi, amma hakan ya zo da tsaiko, domin an fara buga na bogi a kasar nan.

Rahoton da muka hada ya bayyana yadda za ku bambance kudin bogi da na gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.