Gwamnan Zamfara Ya F a Makoki Yayin da Jirgin NAF Yayi Luguden Wuta Kan Farar Hula

Gwamnan Zamfara Ya F a Makoki Yayin da Jirgin NAF Yayi Luguden Wuta Kan Farar Hula

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana alhininsa kan yadda sojin saman Najeriya suka musu barna sakamakon musayar wuta tsakaninsu da 'yan bindiga
  • Hakan ya faru ne sakamakon luguden wutar da NAF tayi wa 'yan bindiga, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu daga cikin mazauna karamar hukumar
  • Gwamnan ya jajantawa iyalan wadanda suka samu raunuka tare da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da alkawarin bincike don gudun sake aukuwar lamarin

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mazauna yankin da suka rasa rayukansu yayin musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da 'yan bindiga a karamar hukumar Maru ta jihar.

Jirgin yakin sojoji
Gwamnan Zamfara Ya F a Makoki Yayin da Jirgin NAF Yayi Luguden Wuta Kan Farar Hula. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, Gwamnan ya bayyana alhininsa game da aukuwar lamarin a wata takarda da mai bashi shawara ta musamman a lamurran da suka shafi sadarwa, Zailani Bappa, ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jarumta: Yadda budurwa ta lallasa 'yan bindiga masu AK47, ta ceto mutum 3 a hannunsu

Bappa ya ce gwamnan yayi takaicin jin labarin mara dadi yayin da sojin saman Najeriya suka yi fito na fito don sheke kungiyar 'yan bindiga, amma cikin rashin sa a hakan ya ritsa da wasu mazauna yankin.

"Wannan lamarin mara dadi yazo ne a lokaci daya, yayin da sojin saman Najeriya suka fito gaba gadi don kawo karshen ayyukan 'yan bindiga, musamman ta hanyar yi musu luguden wuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Zan so a madadin kaina da iyalina, da gwamnatin jiha da dukkan al'ummar jihar Zamfara in mika sakon jaje ga wadanda suka samu raunuka da mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan barnar.”

- A cewar gwamnan.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar tayi hobbasa don ganin ta shawo kan matsalar da hanzarta sanin musabbabin lamarin don gudun sake aukuwar lamarin a gaba.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Dakaru Sun Sheke Hatsabibin Ɗan Bindiga da Yaransa 12 da Suka Addabi Jihohin Arewa 4

Jiragen NAF Sun Ragargaji ‘yan Ta’adda 69 a Zamfara

A Wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya sun kai samame kan ‘yan bindiga da suke addabar jama’a a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Wannan ya biyo bayan daukin gaggawa da jiragen yakin sojin suka kai bayan ‘yan bindiga sun tare babban titin Gusau zuwa Dansadau domin garkuwa da matafiya a kan babban titin.

Tuni sojin suka ragargaje su tare da aike wasu daga ciki barzahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng