Hukumar Shirya Jarrabawa Ta JAMB Ta Fitar da Jadawalin UTME Na 2023

Hukumar Shirya Jarrabawa Ta JAMB Ta Fitar da Jadawalin UTME Na 2023

  • Hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ta bayyana jadawalinta na shirin 2023, za a fara jarrabawar UTME a watan Afrilu.
  • Hakazalika, hukumar ta sanya ranar da za a fara rajistar JAMB da DE, da kuma shirye-shiryen hukumar a gaba
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatu da kungoyiyin malaman jami'a, ana son kara daukar dalibai

FCT, Abuja - jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta ayyana ranar 29 ga watan Afrilun badi a matsayin ranar gudanar jarrabawar UTME a shekarar 2023.

Za a kammala jarrabawar ta UTME a ranar 12 ga watan Mayun 2023, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Hakazalika, hukumar ta kuma sanya ranar 16 ga watan Maris a matsayin ranar gudanar jarrabawar gwaji gabanin jarrabawar ta gaske da za a gudanar.

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

JAMB ta fitar da jadawalinta na 2023
Hukumar Shirya Jarrabawa Ta JAMB Ta Fitar da Jadawalin UTME Na 2023 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Batun rajista kuwa, za a fara tun ranar 14 ga watan Janairun 2023, za a kammala a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar; wata guda kenan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rajistar DE kuwa, za a fara a ranar 20 ga watan Fabrairu, za a kammala a ranar 20 ga watan Afrilun shekarar.

Wannan na kadan daga abin da hukumar ta yanke a ranar Talata 20 ga watan Disamba yayin wani zaman masu ruwa da tsaki da aka gudanar.

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Buhari da ASUU

Wannan sanarwa na JAMB na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai ruwa rana da kungiyar malaman jami'a ta ASUU da CONUA kan batun rike albashin ma'akata.

Idan baku manta ba, kungiyar malaman jami'a ta shafe watanni sama da 8 tana yajin aiki biyo bayan rashin biya musu bukatunsu.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Dakaru Sun Sheke Hatsabibin Ɗan Bindiga da Yaransa 12 da Suka Addabi Jihohin Arewa 4

Ya zuwa yanzu, malaman sun janye yajin aikin, amma ana ci gaba da rikici tsakanin kungiyoyin jami'oin.

Har yanzu, wasu jami'o'in Najeriya basu kammala daidaita tsarin karatun shekarar 2021 da 2022 ba, ga kuma 2023 na shirin shiga, JAMB ta sanar da lokacin jarrabawa.

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya bayyana cewa, yana da mafita mai kyau game da yawan yajin aikin ASUU.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa, zai biya dukkan bukatun kungiyar malaman jami'a idan aka zabe a matsayin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.