Bidiyon Wata Amarya da Ta Zo Wurin Daurin Aurenta Da Rauni Ya Jika Zukatan Jama’a
- Wata kyakkyawar budurwa da aka yiwa aiki a gwiwa ta nuna babu abin da zai hana faruwar aurenta
- Wani bidiyon da aka yada a TikTok, mutane sama da 1.5 ne suka kalle shi ya zuwa ranar Talata 20 ga watan Disamba
- Jama'ar kafafen sada zumunta sun yi ca kan bidiyon, sun bayyana kalamai masu jika zuciya game da wannan amarya
Wata mata ta yada wani bidiyon aurenta, ya samu karbuwa a idon jama’a, mutum miliyan 1.5 ne suka kalli bidiyon ya zuwa ranar Talata 20 ga watan Disamba.
Matar mai suna Marta ta ce an yi mata aikin gwiwa a asibiti, amma duk da haka tace sam ba za a daga bikinta ba.
Marta ta ce, an yi mata aikin ne wata guda kafin aurenta, kuma bata warke ba haka ta halarci wurin bikin aurenta.
Bidiyon mai dakiku 9 ya nuna lokacin da matar ke rike da sanda ga kuma wasu suna taimaka a wajen auren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafarta ta hagu ne ta samu matsala, kamar yadda ya bayyana a bidiyon, kuma alamu na nuna bata warkw ba har yanzu.
Sakon da Marta ta wallafa
Ta bayyana cewa:
"Soyayya na da kyau da kuma karfi idan ana yi wa da mutumin da ya dace. An yi min aiki gwiwa wata daya kafin aure na amma ina son murnan bikin duk da kuwa ciwon da nake fama dashi, ba zan taba mantawa da wannan rana ba.”
Abin da babu shakka akai shine, Marta ta yi kyau sosai a ranar bikin, kuma jama’ar TikTok sun yi martani mai ban mamaki.
Kalli bidiyon:
Ga kadan daga abin da jama’a ke cewa
@user5273245473361:
"Ina taya ki murna, gaskiya kun yi kyau dukkanku.”
@lenatlanta2019:
"Ina taya ki murna. Soyayyar gaskiya kenan.”
@Jenny Pinckney Hunt:
"Ya yi kyau sosai.”
@Queenvee341:
"Kin yi kyau. Ina taya ki murna.”
@Akran Berhane:
"Ina taya ki murna Marta bisa shagalin bikinki, kuma ina fatan ki samu sauki nan kusa.”
@Fathi Fathi:
"Tsananin soyayya da mutunta juna.”
Ya fasa aure bayan gano sirrin budurwarsa
A wani labarin kuma, ango ya fasa auren budurwarsa bayan gano wani sirri da ta boye masa, tana da 'ya'ya har biyu bai sani ba.
Jama'ar kafar sada zumunta sun yi martani mai zafi game da wannan lamari, sun ce abin da ya yi daidai ne kuma a lokacin da ya dace.
Ana yawan samun rikici da rashin fahimta tsakanin ma'aurata, lamarin da ke jawo shari'a da cece-kuce a cikin al'umma.
Asali: Legit.ng