Majalisar Dattijai Ta Tabbatar Da Nadin Babban Mukami Ga Wacce Buhari Ya Zaba

Majalisar Dattijai Ta Tabbatar Da Nadin Babban Mukami Ga Wacce Buhari Ya Zaba

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin hadimar shugaban kasa Lauretta Ifeanyi-Onochie a matsayin shugaban kwamitin NDDC
  • Hakan na zuwa ne bayan kwamitin Neja Delta na majalisar wakilai na tarayya da na dattawa sun tantance jerin sunayen wadanda Buhari ya tura don nadin
  • Baya ga Onochie, majalisar ta kuma tabbatar da nadin wasu mutane 12 da Shugaba Buhari ya tura sunayensu domin nadin a NDDC

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin hadimar shugaban kasa kan sabbin kafofin watsa labarai, Lauretta Ifeanyi-Onochie, a matsayin shugaban kwamitin ci gaban yankin Neja Delta, rahoton The Punch.

Majalisar ta tabbatar da hadimar wacce ake ta kai ruwa rana kanta tare da wasu zababbun mutanen 12 bayan ciyaman din kwamitin Neja Delta na Majalisa, Amos Bulus, ya gabatar da rahoto a ranar Talata, 20 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Shugaba Buhari Ya Gana da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2

Onochie
Majalisar Dattijai Ta Tabbatar Da Nadin Babban Mukami Ga Wacce Buhari Ya Zaba. Hoto: @daily_trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunda farko, Shugaba Buhari ya mika sunayen wadanda ya zaba ga majalisa domin su tabbatar da nadinsu bisa tanadin sashi na 2(2)(a) na dokar NDDC.

Kwamitocin Neja Delta na majalisar wakilai na tarayya da majalisar dattawa duk sun tantance wadanda aka zaba kafin tabbatar da su, rahoton The Cable.

Buhari ya tura sunayen wadanda aka zaba a hukumar NDDC zuwa majalisar dattijai sau 2 don tabbatarwa, an aika da jerin farko zuwa majalisar dattijai a shekarar 2021, kuma an tantance su kuma an tabbatar da su.

Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ya ce Buhari ya sake tura sunayen wadanda aka zaba din ne don tabbatar da su saboda kura-kurai a sunayen na farko.

An yi jayayya game da nadin Onochie tsakanin mambobin kwamitin inda wasu suka ce ba daga garin da ke samar da man fetur ta fito ba a Jihar Delta.

Kara karanta wannan

Allah Yayi wa Alhaji Shehu Malami, Fitaccen 'Dan Kasuwa Kuma Yariman Sokoto, Rasuwa

Sun ce wannan dalilin shine ya sa bai kamata a nada ta ba duba da cewa ya ci karo da dokar NDDC, wanda ya hana a nada ta shugabancin hukumar

Buhari ya nada Salihu Abdulhamid a matsayin sabon direktan NTA na kasa

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Salihu Abdulhamid Dembos a matsayin sabon shugaban gidan talabijin na kasa, NTA.

Lai Mohammed, ministan sadarwa da al'adu na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a birnin tarayya, Abuja.

Dembos shine direktan sashin kasuwanci na NTA kafin a yi masa nadin shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164