Mummunan Hatsari ya Lashe Rayukan Mata da Kananan Yara 11 a Hanyar Kano Zuwa Zaria

Mummunan Hatsari ya Lashe Rayukan Mata da Kananan Yara 11 a Hanyar Kano Zuwa Zaria

  • A kalla mata 11 da yara ne suka rasa rayukansu sanadiyyar mummunan hatsarin da ya auku a babban titin hanyar Kano zuwa Zaria
  • Ganau ya bayyana yadda motar kaya kirar Hilux ta murkushe Toyota bus wanda hakan yasa ta kifa gefen titi gami da kamawa da wuta
  • An tabbatar da tsirar mutane shida, yayin da sauran suka kone kurmus wadanda dukkansu mata ne da yara

Kano - A rahoton da aka samu, a kalla mata 11 da yara sun rasa ransa a hatsarin mota kan babban titin hanyar Kano zuwa Zaria.

Hatsarin Mota
Mummunan Hatsari ya Lashe Rayukan Mata da Kananan Yara 11 a Hanyar Kano Zuwa Zaria. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro yadda lamarin ya auku a yammacin Asabar misalin karfe 5:00 wanda ya shafi motar bus kirar Toyota C20 da motar kaya kirar Hilux.

Ganau ya bayyana yadda:

"Motar kaya kirar Hilux dake tahowa daga Kano zuwa Zaria ke bin bayan bus din da gudu, tare da son shiga gaban bus din, amma cikin rashin sa'a akwai wata mota mai tahowa, wacce ta sanya direban dakatawa.

Kara karanta wannan

Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Zaiyi Zabe A Kurkuki, Sakamakon Umarnin Kotu Na A Tsareshi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yayin dawowa daga shiga gaban, direban Hilux din ya murkushe Toyota bus din, wanda hakan yasa ta kifa kasan titin gami da kamawa da wuta.
"Baya ga mutane shida da suka tsira, mun kirga gawawwaki 11 da suka kama da wuta, dukkansu mata ne duk da kananan yara."

Yayin zantawa da Daily Trust, Malam Abdulaziz Isiyaku, wanda ya rasa 'ya'yansa biyu mata - Zainab mai shekaru 16 da Aisha mai shekaru 8 - ya ce marigayan na dawowa ne Zaria daga Kano bayan ziyartar 'yan uwansu.

"Muna sa ran dawowarsu gida misalin karfe 6:00 na yamma, sai dai da bamu gansu ba, muka kira 'yan uwanmu a Kano, inda suka shaida mana cewa sun shiga motar zuwa Zaria.
"Na fara kiraye-kirayen waya, inda aka shaidamin hatsarin da suka tafka kan hanyarsu, hakan yasa na taho, duk da sun kone kurmus, na iya gane gawawwakinsu."

Kara karanta wannan

Jarumta: Yadda budurwa ta lallasa 'yan bindiga masu AK47, ta ceto mutum 3 a hannunsu

- A cewarsa.

Yayin da aka tuntubi kakakin hukumar kula da tituna na tarayya ta wayarsa don tsokaci game da hatsarin, ya ce baya gari saboda haka ba zai iya cewa komai ba game da lamarin.

Mota ta fada rafi a garin Gwarzo

A wani labari na daban, wata mota dauke da fasinjoji ta fada rafi a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.

An samu damar ceto wasu da ransu yayin da aka tsamo wasu gawawwaki inda ake cigaba da neman wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng