Rayuka 9 Sun Salwanta Yayin da Mota Cike da Fasinjoji ta Fada Rafi a Kano

Rayuka 9 Sun Salwanta Yayin da Mota Cike da Fasinjoji ta Fada Rafi a Kano

  • Rayuka 9 sun salwanta yayin da wata mota kirar Golf Wagon ta fada wani ruwa dake karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano
  • An gano cewa, motar dankare da fasinjoji 12 ta fada ruwan yayin da take hanyar zuwa Katsina daga Kano cike da mata, maza da kananan yara
  • Masu ceto sun fada inda suka samo mutum 11 daga ciki inda aka tabbatar da mutuwar 9 a ciki sannan ba a riga an tsamo dayan ba

Kano - Mutane tara da suka hau wata mota kirar Golf Wagon sun rasa rayukansu a karamar hukumar Gwarzo dake Kano yayin da motar ta fada wani ruwa, jaridar Punch ta rahoto.

Gwarzo Dam
Rayuka 9 Sun Salwanta Yayin da Mota Cike da Fasinjoji ta Fada Rafi a Kano. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan kwana-kwana na jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace:

“A ranar Asabar, 19 Nuwamban 2022, hukumar kwana-kwana ta jihar ta samu kiran gaggawa daga wani Ali Faci wurin karfe 6:45 na yamma.

Kara karanta wannan

EFCC ta sha Alwashin Gwangwaje Duk Wanda ya Fallasa Boyayyin Kudi da 5% na Jimillarsu

“Faci ya sanar da cewa wani lamari ya faru a dam din Fada dake karamar hukumar Gwarzo kan titin Dayi inda ya kara da cewa masu kashe gobara dake Gwarzo sun isa wurin karfe 7:10 na yamma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Sun gano cewa wata mota kirar Golf Wagon mara rijista daga Kano tana kan hanyarta ta zuwa Katsina ta zunduma cikin Fada dam. An ceto mutum 12 da har yanzu ba a tantance sunayensu ba.
“Wadanda hatsarin ya ritsa dasu sun hada da yara mata biyu masu watanni shida shida a duniya, mata hudu masu shekaru 30,28,27 da 25 tare da maza shida masu kimanin shekaru 48, 45, 42, 40, 35 da 28 a duniya.

Masunta sun taimaka wurin tsamo su

Tare da taimakon masunta, ‘yan kwana-kwanan sun yi nasarar ceto mutane uku da ransu yayin da sauran taran basu san inda kansu yake ba.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro Sun Damke Mai Garkuwa da Mutane Yana Tsaka da Siyan Abinci a Kwara

Channels TV ta rahoto cewa, yayin da aka mika su babban asibitin Gwarzo domin samun agajin likitoci, an tabbatar da mutuwarsu.

Kamar yadda ganau ya bayyana, daya daga cikin mutanen da suka fada har yanzu yana cikin ruwan inda yayi alkawarin za a cigaba da nemansu har sai an ceto shi.

Hatsari ya lashe rayuka a Kano

Rayuka 9 sun salwanta yayin da wasu uku suka jigata sakamakon hatsarin mota da ya ritsa dasu a jihar Kano.

Hatsari ya auku ne bayan wata tirela ta latse karamar motar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel