Taraba: Mata Sun ce Ba Za a Barsu a Baya Ba, Sun Shiga Farautar 'Yan Bindiga

Taraba: Mata Sun ce Ba Za a Barsu a Baya Ba, Sun Shiga Farautar 'Yan Bindiga

  • A halin yanzu, mata mafarauta suna ta tururuwar hada kai da 'yan uwansu mafarauta maza don yakar 'yan bindiga a jihar Taraba
  • Bincike ya bayyana yadda matan aure da 'yan mata da dama suka shiga kungiyar mafarautan don bada tasu gudunmawar wajen yakar 'yan bindiga
  • Shugabar kungiyar ta bayyana manyan dalilan da yasa suka yi hobbasa duba da yadda 'yan bindiga suka halaka musu mazaje, sacewa da bata mata

Taraba - Mata mafarauta sun hada kai da 'yan uwansu maza don yakar 'yan bindiga a jihar Taraba.

Bincike ya bayyana yadda matan aure da 'yan mata da dama a yanzu suka shiga kungiyar mafarauta, wadanda ke bada gudunmawa wajen yakar 'yan bindiga a fadin kasar.

Taswirar Taraba
Taraba: Mata Sun ce Ba Za a Barsu a Baya Ba, Sun Shiga Farautar 'Yan Bindiga. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wata mafarauciya, Hauwa Lawal, ta bayyanawa City & Crime yadda suka shiga kungiyar mafarauta don taimakawa wajen yaki da ayyukan 'yan bindiga a jihar.

Kara karanta wannan

Jarumta: Yadda budurwa ta lallasa 'yan bindiga masu AK47, ta ceto mutum 3 a hannunsu

A cewarta, 'yan bindiga sun halaka mutane da dama duk da mazajensu da yara a yankuna da dama na jihar, yayin da aka yi garkuwa da yara mata da matan aure da aka sace gami da yi musu fyade a yankin Karim zuwa Lamido, Gassol da karamar hukumar Bali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, miyagun ayyukan da 'yan bindiga sukewa mata ne ya tilasta mata da dama shiga kungiyar mafarautan don yaki da 'yan bindiga a cikin jihar.

Karfafawa gami da kokarin mata don yaki da 'yan bindiga ne yayi sanadiyyar rantsar da Habiba Isa a matsayin shugabar mafarauta mata na yankun Arewa masi gabas.

Shugabar matan jin kadan bayan rantsar da ita da shugaban kungiyar mafarauta na kasa, Umar Muhammad Tola yayi, a Zing ta ce, a yanzu an san da zaman mafarauta mata a kungiyar da maza ne suka fi yawa.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An yi jana'izar wasu ma'aurata da 'yan bindiga suka kashe bayan karbe kudin fansa N7.5m

Ta ce mafarauta mata suna da jarumta da shirin taimakawa wajen yakar 'yan bindiga, inda ta kara da cewa, mafarauta mata suna taka babbar rawa wajen yaki da Boko-Haram a baya da kuma yanzu.

"Mun gaji farauta daga kaka da kakanninmu yayin da mata da yawa suka shiga kungiyar mafarautan a matsayin gudunmawarsu don tseratar da anguwanninmu da kauyukanmu daga ayyukan 'yan bindiga."

- A cewarta.

'Yan ta'adda sun kai farmaki kudancin Kaduna, sun sheke 28

A wani labari na daban, wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki yankin kudancin Kaduna a karamar hukumar Kaura ta Kaduna.

Sun halaka mutane da yawa a garuruwan Malagum 1 da Sokwong.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng