Nan Ba Da Dadewa Ba Zamu Ceto Leah Sharibu, Ministar Buhari

Nan Ba Da Dadewa Ba Zamu Ceto Leah Sharibu, Ministar Buhari

  • Ministar harkokin mata ta bayyana irin gudunmuwar da gwamnatin tarayya ke baiwa iyayen Leah Sharibu
  • Sharibu na cikin daliban mata yan makarantar GGSS Daphi da yan ta'adda suka sace a shekarar 2018
  • Gwamnati ta samu nasarar ceto mafi akasarin yan matan amma yan ta'addan suka rike Sharibu

Abuja - Sama da shekaru biyar bayan yan ta'addan Boko Haram suka yi awon gaba da dalibar makaranta, Leah Sharibu, har yanzu gwamnati bata samu nasarar ceto ta ba.

Gwamnatin tarayya ta ce bata daina kokarin ceto ta ba kuma tana taimakawa iyayenta iyakan gwargwado.

Ministar harkokin Mata, Dame Pauline Tallen, ta bayyana hakan yayin hira da manema labarai kan nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu karkashin ma'aikatarta, rahoton Vanguard.

Dame Pauline Tallen, wacce ke tare da Ministan labarai, Lai Mohammed, a taron ta bayyana cewa duk da rashin iya ceto Leah Sharibu duk shekarun nan, suna taimakawa iyayenta don rage musu zafi.

Kara karanta wannan

Minista Ta Gagara Rike Hawaye, Ta Fashe da Kuka Kan ‘Yan Matan da B/Haram Suka Dauke

Tace:

"Ina taimaka musu a duk kafar da na samu. Ina tabbatar muku cewa duk bukatar da na gabatar na iyayen Leah gaban Shugaban kasa yana amincewa. Ina da hotunan jirgin da jami'an tsaro da Buhari ya bani na tafi ganinsu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dame Pauline Tallen
Nan Ba Da Dadewa Ba Zamu Ceto Leah Sharibu, Ministar Buhari
Asali: Twitter

Game da sauran yan matan Chibok dake hannun yan ta'addan har yanzu, Dame Pauline Tallen, ta ce gwamnati ba za tayi kasa a gwiwa wajen ganin ta cetosu ba.

Ta ce a matsayinta na Uwa, ba karamin bacin rai ne gareta wadannan yan mata na hannun yan ta'adda ba.

Tace:

"Muna iyakan kokarinmu wajen ceto sauran yan matan Chibok dake hannun yan ta'adda. Shugaban kasa na sane da abinda yake faruwa.

Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi fa ya ya yiwa Najeriya iyakan kokarin da zai iya cikin shekarun bakwan da ya mulki kasar nan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Jama'a suna ta mutuwa bayan cin abinci mai guba a wata karamar hukuma

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a birnin Washington DC, kasar Amurka yayin halartan taron hadin kasa Amurka da nahiyar Afrika makon da ya gabata.

Buhari ya bayyana cewa idan ya sauka daga mulki zai huta sosai saboda ya aikatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida