'Yan Sanda Sun Halaka Kasurgumin Dan Garkuwa da Mambobinsa a Bauchi
- Gwarazan jami'an 'yan sanda sun samu nasarar sheke shugaban tawagar yan bindiga, Madaki Mansur, da wasu mambobin tawagarsa 12
- A wata sanarwa da kakakin 'yan sandan Bauchi ya fitar ranar Litinin yace sun kwato makamai da kayan aikin 'yan ta'addan
- A halin yanzun gamayyar jami'an tsaro sun baza komarsu domin cafke ragowar yan bindigan da suka tsere yayin musayar wuta
Bauchi - Dakarun rundunar yan sandan jihar Bauchi sun halaka kasurgumin mai garkuwa da mutane, Madaki Mansur, da wasu yan bindiga 12.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ana zargin yan bindigan da hana zaman lafiya a yankin ƙaramar hukumar Alkaleri, Bauchi da makotan jihohi kamar Taraba, Filato da Gombe.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Bauchi ranar Litinin.
Ya ce an yi kazamar musayar wuta kuma sakamakon haka ne dakaru suka tura masu garkuwa 12 barzahu yayin da sauran suka sa ƙafa zuwa dazuka cikin mawuyacin hali.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A kokarin da muke yi na haɗin guiwa wajen ganin mun kakkaɓe ayyukan ta'addancin 'yan bindiga a Bauchi, musamman a ƙaramar hukumar Alkaleri, rundunar yan sanda ta samu nasarori kwanan nan."
"A ranar 19 ga watan Disamba, 2022 da karfe 2:30 na rana gamayyar dakarun tsaro suka bude wa yan bindigan/masu garkuwa da mutane wuta a mafakarsu huɗu, Mansur, Digare, Gwana da Dajin Madam duk a Jejin Alkaleri."
"Bayan zazzafar musayar wuta, luguden wutan jami'an tsaro ya sheka 'yan bindiga 12 barzahu yayin da sauran suka tarwatse suka gudu cikin yanayi da raunukan harbi."
Jami'ai sun kwato kayan aiki
A ruwayar Punch, SP Wakil ya bayyana cewa gamayyar jami'an tsaron sun kwato makamai da Baburan aiki na yan ta'addan yayin musayar wuta.
"A halin yanzun rundunar yan sanda ta baza komarta ta ko ina da nufin damko waɗanda suka tsere."
A wani labarin kuma Jirgin Yakin Soji Ya Saki Bam a Wani Gari a Zamfara, Sama da Mutane 60 Sun Rasu
Mazauna ƙauyen Mutumji sun shaida cewa ma fi yawan waɗanda suka mutu yan ta'adda ne amma samamen sojin ya haɗa da wasu fararen hula.
Wani mamban ƙungiyar kare hakkin ɗan adam kuma mazuanin yankin ya ce yanzu haka an tafi mutane 12 da suka jikkata Asibitin Gusau.
Asali: Legit.ng