Jigawa: Gobara ta Lamushe Bukka, Ta Hade da ‘Ya’ya 2 da Mahaifiyarsu
- Wata mummunar gobara ta lashe rayukan wata mata mai shekaru 30, Khadija Ibrahim da 'ya'yanta mata biyu a kauyen Tsangarwa na karamar hukumar Gwaram dake jihar Jigawa
- Lamarin ya auku ne misalin karfe 11:00 na daren Juma'a, inda aka ga bukkar da suke ciki tana ci da wuta, yayin da suke bacci
- Duk da ba a tabbatar da masabbabin gobarar ba, amma makwabta sun ce bata rasa nasaba da rushin da suka kai daki don shan dumi
Jigawa - Wata mata mai shekaru 30, Khadija Ibrahim da 'ya'yanta mata biyu sun rasa rayukansu a wata gobara da ta auku a kauyen Tsangarwa na karamar hukumar Gwaram dake jihar Jigawa.
Jaridar Punch ta rahoto cewa, kamar yadda takardar da kakakin jami'an tsaron farin kaya na jihar, Adamu Shehu ya bayyana, lamarin ya suku a ranar Juma'a misalin karfe 11:00 na dare yayin da gobarar ta fara cin bukkar da marigayan ke bacci.
Kamar yadda takardar ta bayyana:
"Gobara ta kama wata bukka, inda wata mata mai shekaru 30 da yaranta mata biyu, Aisha mai shekaru hudu da Rabi mai shekaru biyu suka rasa rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Har yanzu ba a san musabbabin gobarar ba, amma makwabta sun ce ba zai wuce rushin da suka kai bukkan don shan dumi ba.”
Sai dai, kamar yadda takardar ta bayyana, an garzaya da wadanda lamarin ya auku dasu asibiti mafi kusa inda likitocin dake sashin gaggawa na asibitin suka tabbatar da mutuwarsu, inda ba a jinkirta yin jana'izarsu ba kamar yadda Musulunci ya tanada.
Gobara ta tashi a kasuwar Singer dake Kano
A wani labari na daban, mummunar Gobara ta tashi a kasuwar Singer dake kwaryar birnin Kano dake Najeriya.
Kasuwar dai ta shahara wurin siyar da Kayayyakin masarufi na amfanin gida da suka hada da shinkafa, taliya, madara, gero, dasa da sauransu.
Gobarar ta lashi wasu ma’adanan kayayyakin ‘yan kasuwar ne wanda lamarin ya matukar tada hankulan jama’a.
Tuni aka nemi daukin jami’an kwana-kwana inda suka garzaya tare da yin duk kokarin da ya dace wurin kashe gobarar dake barazanar hadawa da shaguna masu tarin yawa.
Asali: Legit.ng