Nasara: Hatsabibin Dan Bindigan da Aka Fi Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Hannu
- An Kama wani kasurgimin ɗan bindiga da ya hana zaman lafiya a wasu yankunan jihar Anambra
- Dakarun JTF ne suka yi ram da mutumin mai suna, Chuma Ejionye, bayan samun wasu bayanan sirri da daren jiya
- Rundunar yan sanda reshen jihar tace har yanzun rahoton wannan nasara ba ta isa hannunta ba
Anambra - Wani kasurgumin ɗan bindiga da aka jima ana nema ruwa a Jallo ya shiga hannu, Jami'an tsaro 'Yan Bijilanti ne suka kama shi a garin Ezinifitte, karamar hukumar Nnewi ta kudu a Anambra.
Wanda ake zargin mai suna, Chuma Ejionye, ɗan asalin garin Ezinifitte, ana ganin shi ke ɗaukar nauyin kai hare-haren ƙona wurare a faɗin yankin ƙaramar hukumar Nnewi ta kudu.
Kewayen Nnewi ta kudu musamman garuruwan Ukpor, Ezinifitte da Unubi sun jima ana musu kallon maɓoyar masu aikata muggan laifuka da 'yan bindiga lokacin da rashin tsaro ya fi muni a Anambra.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa a wani bidiyo dake yawo a Soshiyal midiya, wanda ake zargin ya yi ikirarin an fi saninsa da sunan, "Small Case."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Da farko ina sansanin Unubi, daga baya na koma Ezinifitte kafin daga bisani na koma Agulezechukwu inda na zauna da sauran mambobin tawaga. Daga baya na tsere domin kafa tawa dabar."
A cewar bidiyon, hatsabibin ɗan bindigan ya jima a cikin jerin waɗan da jami'an tsaro masu aikin haɗin guiwa a Anambra ke nema ruwa a jallo.
"Shahararren mai garkuwa da mutane ne kuma yana da hannu a kashe-kashen jami'an tsaro har da Yan bijilanti. Ya taɓa garkuwa da babban mutum ya karɓi miliyan ɗaya da rabi kafin ya sake shi."
"Bisa rashin sa'a suka jefar da mutumin a wani wuri, ya samu matsala a huhunsa har yanzu yana jinya. Dakarun JTF sun je gidan wanda ake zargi sun samu bindigu da kayan jami'an tsaro."
"Ya jima cikin waɗanda ake nema ruwa a jallo kuma yana cikin hatsabibin da suka jawo ake kallon Ezinifitte da Nnewi ta arewa a matsayin wuri mai haɗari. Jiya muka samu bayanan sirri muka kama shi."
- A cewar mai bayani a cikin bidiyon.
Yayin da aka tunfube shi, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda reshen jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, yace babu wani rahoto makamancin haka da ya isa ofishinsa.
Yan Bindiga Sun Aike da Wasika Zuwa Garuruwa Hudu, Sun Faɗi Lokacin Kai Hari
A wani labarin kuma Wasu miyagun da ake tsammanin makiyaya ne sun aika wasi garuruwa huɗu a jihar Ogun
A wasikar, maharan sun gaya wa mazauna yankin su tsammaci zuwansu ko da wane lokaci a yanzun domin ba zasu lamurci cin kashin da ake wa yan uwansu ba.
Sun kuma gargaɗi shugabannin al'umma a garuruwan cewa su jira zuwansu, zasu zo karban kadarorin iyayensu da aka kwace.
Asali: Legit.ng