Ku Inganta Rayuwar Mutane Shine Mafi A'ala Mai Makon GIna Gadojin Sama

Ku Inganta Rayuwar Mutane Shine Mafi A'ala Mai Makon GIna Gadojin Sama

  • Ku bunkasa harkokin ilimi da ilimantarwa yafi ku gina filai oba, ilimi ne zai magance jahilici ya kawo tsaro a cikin al'umma inji Gumi.
  • Gwamanatoci na maida hankali kan yin wani aiki da za'a gani a yaba, maimakon su gina al'umma su sami tsaftar zuciya.
  • Mutane sun fi bukatar ilimi maimakon amfani da karfi wajen magance matsaltsalon da suka damesu

Kaduna: Shehin malamin addinin islama a Nigeria, kuma dan gidan fittacen malamin tafrsirin nan, Sheikh Abubakar Mahmud yace bunkasa ilimi shi ne zai kawo zaman lafiya mai dorewa akan gina gadojin sama.

Malamin ya ce rashin tsaro da ake gani a Nigeria yana watangaririya ne a tsakanin talauci, jahilci da kuma rashin adalcin shuwagabbanni.

Shiek Gumi
Ku Inganta Rayuwar Mutane Shine Mafi A'ala Mai Makon GIna Gadojin Sama Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A wata hira da jaridar SundaySun tayi da malamin yace ya kamata gwamnati ta sake tunani kan abubuwan da mutane suke bukata wanda zasu binkasa harkokin ilimi.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Sheke Tsohuwa Mai Shekaru 120 tare da Wasu 5

Malamin yace indai 'yan kasa basu samu ilimi ba, to dole rashin tsaro sabida jahilci ne ke rura wutar rikici da rashin aikinyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya kamata mu sani, Almajirci wata hanya ce ta samun karatu kamar kowa, sai dai kuma in wani kallo kake masa, amma wai ace za'a soke ko daina shi ba zai haifar da wani 'da mai ido ba"
"Almajirci wata hanya ce ta neman ilimi da ta shude, kamar amfani da jaki wajen da rakumi wajen tafiye-tafiye, wanda yanzu aka canjasu dana zamani"
"Idan ka wadata mutane da abubuwan zamani, to mutane zasu bar wancan din. Bari na fada maka har yanzu wasu mutane a kauyuka na amfani da jaki da rakumi wajen yin tafiye-tafiye"
“Kalli, idan gwamnatoci zasu gina makarantu masu kyau, da kuma inganta harkokin ilimin, mai zai sa ace mutane zasu samu ilimi da wayewar da gwamnati ke bukata ba"

Kara karanta wannan

Jami'an Rundunar Tsaron Farin Kaya DSS, Sunyi Gaba Da Babban Dalibin Abdul-Jabbar Sabida Sabawa Dokar Zaman Kotu

"Ku zuba kudi sosai a harkar ilimi maimakon gina manyan gadoji"

Kamar yadda awolawo yayi a yakin yarabawa, zan iya tuna taken "ilimi kyauta". Kuma yace ba abinda mutane suke bukata sama samar musu da ilimi mai nagarta"

"Idan ba ka koyawa, mutane wani muhimmin abu wanda ya shafi ilimi da sana'o'in dogaro da kai ba ka barsu sun gararamba ta yaya zasu rayu koda kace zaka basu kudi a karshen wata"

Jaridar The Cable ta rawaito cewa gumi na wannan batun ne kan batun zaben shekarar 2023 da kuma wanda ya dace a zaba.

Gumi Yace Katin Zabe Yafi Muhimmanci Sama da Komai

A wani labarin mai kama da wannan kuma shehin malamin yayi kira ga 'yan Nigeria game da zaben shekarar 2023 da wanda ya kamata a zaba.

Shehin malamin yace dole ne 'yan kasa su sani katin zabensu a yanzu ya fiye musu muhimmanci sama da duk wata takardar sheda katin fasfo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel