‘Yan Ta’adda na Koyar da ‘Ya’Yansu Ta’addanci Don Su Addabi Kasa nan Gaba, Kwamandan OPHK
- Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Christopher Musa ya bayyana cewa ‘yan ta’adda suna hora ‘ya’yansu domin dasawa daga inda suka tsaya
- Sai dai ya sanar da cewa a kalla ‘yan ta’adda 83,000 ne suka tuba tare da mika wuya ga jami’an tsaro amma ciki 41,000 duk kananan yara ne
- Musa ya sanar da cewa sun shirya dawo da zaman lafiya kasar nan don haka COAS yana saukaka musu aiki inda suke dagewa
Yobe - Christopher Musa, kwamandan rundunar Operation Hari Kai, ya sanar da cewa a kalla mayakan ta’addanci na Boko Haram 83,000 ne suka mika wuya ga rundunar sojin Najeriya.
A yayin jawabi a ranar Juma’a yayin ziyarar da ya kaiwa Mai Mala Buni, Gwamnan jihar Yobe, Musa yace ‘yan ta’addan da suka mika wuya suna wuraren gyara hali dake fadin kasar nan.
Kwamandan yace 41,000 daga cikin ‘yan ta’addan da suka tuba duk yara ne da aka horar don su zama mayakan ta’addanci a nan gaba.
“Ubangiji ya tsare mu ba kadan ba, mun samu tubabbun ‘yan ta’adda masu yawa. Muna gangara har kusa da 83,000 kuma daga cikinsu 41,000 duk kananan yara ne.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Musa yace.
‘Yan ta’addan suna kokarin kawo wasu sabbin ‘yan ta’addan, yaransu wadanda da sun kasance masu matukar hatsari saboda ka san yara yadda suke, abinda suka ga ana yi ne suke kwafa.
“Toh idan suka girma kuma suna tunanin kisa daidai ne, zasu zama masu matukar hatsari.”
- Yace.
Kwamandan yace rundunar sojin da sauran hukumomin tsaro zasu cigaba da tabbatar da ingantattun tsarika wurin kawo karshen ta’addanci.
“Ko ma ya za a yi, ko me ake bukata don zaman lafiya, mun shirya samun shi. Shugaban sojin kasa ya kasance mai matukar bada goyon baya a duk abubuwan da muke kuma hakan yasa aikinmu yake sauki kullum.”
- Yace.
Kwamandan a tattaunawarsa ta baya-bayan nan da jaridar TheCable, yace ‘yan ta’addan suna ta mika wuya saboda suna don yin rayuwa kamar kowa.
Tubabbun ’yan ta’addan Boko Haram sun share tituna
A wani labari na daban, tubabbun ‘yan Boko Haram sun yi aikin tsaftace garin Maiduguri.
Sun hada da neman yafiya daga jama’a kan yadda suka addabesu a baya.
Asali: Legit.ng