Buhari @80: Na Hannun Daman Tinubu Ya Lissafa Manyan Zarge-zargen Da Aka Yiwa Shugaban Najeriya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fuskanci zarge-zarge da dama tun bayan da ya hau mulki a 2015
- Daya daga cikin ikirarin da aka yi shine cewa Buhari ya mutu kuma mutumin da ke Aso Rock Jubrin ne daga Sudan
- Wani hadimin Bola Tinubu, Joe Ibokwe, ya lissafo wasu daga cikin zarge-zargen da magauta suka yi kan Buhari
Watanni bayan ya hau karagar mulki a 2015, Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke bikin cika shekaru 80 a yau Asabar, 17 ga watan Disamba ya fuskanci zarge-zarge daga magautansa.
Koda dai shugaba Buhari ya hau mulki da niyan kawo chanji, mutane da dana suna ganin ya gaza cika alkawaran da ya dauka yayin yakin neman zabensa bayan ya lashe zabe a 2015.
Joe Ibokwe, wani dan kashenin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, ya lissafa wasu zarge-zargen da aka yiwa shugaban kasar.
Kalle su a kasa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Sun fadi abubuwa marasa dadi game da PMB
2. Sun kira shi da sunaye iri-iri
3. Sun ce ba shi da lafiya
4. Sun ce Jibrin ne daga Sudan
5. Sun ce bai san komai ba
6. Sun zarge ahi da bangaranci
7. Sun ce bai da takardar shaidar karatu
8. Sun ce bai samu kowani nasara ba a kusan shekaru 8
9. Sun zage tsawon awanni da dama
10. Sun kira shi da bugharia
11. Sun ce mutumin da ke Aso Rock ba PMB bane
12. Sun ce baya iya magana
Da yake rufe wallafarsa, Igbokwe ya ce:
"Ku kalla a yanzu wannan mutumin ya cika shekaru 80 a yau. Kwanan nan ku ka ga an bude gadar Najeriya ta biyu a ranar 15 ga watan Disambar 2022. Za ku ji shi kuma za ku gan shi."
Na yi iya bakin kokarina a matsayin shugaban kasa, Muhammadu Buhari
A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya tsawon shekaru bakwai da rabi da suka wuce, ya yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya kawo sauyi a kasar.
Buhari wanda ya ce kasar na da girma da tarin mutane masu yawan gaske, ya kuma ce gwamnatinsa na kokarin inganta rayuwar matasa.
Asali: Legit.ng