Wani Dalibin Da Yake Sai Da Biredi Ya Zama Babban Dan Kasuwa, Yana Samun Naira Miliyan 41.5 Duk Shekara

Wani Dalibin Da Yake Sai Da Biredi Ya Zama Babban Dan Kasuwa, Yana Samun Naira Miliyan 41.5 Duk Shekara

  • Wani dalibin makarantar sakandare da ya fara kasuwancin burodi daga baya kuma ya koma saida kayansa ta kafafen sada zumunta, ya zama mai arziki
  • Justin Ellen ya fara samun Naira miliyan 2 duk wata, wanda hakan ya shafi zuwa makarantarsa.
  • Ellen ya ce kafofin sada zumunta sun taka muhimmiyar rawa a kasuwancinsa kuma ya ce yana samun tsakanin dala 5,000 zuwa dala 9,000.

Justin Ellen dan shekara 17, ya shiga tsaka mai wuya inda ya raba hankalinsa kan neman kudi ko kuma zuwa jama'a.

Dalibin na tunanin ko zai ci gaba da yin sana'ar burodi, ko kuma ya je jami'a don ci gaba da karatunsa .

Matashin dai shine matashin nan wanda yai takara a shahararren wasan nan na "Gashin biredi" na kamfanin Netflix.

Kara karanta wannan

"Ko ka zabi APC ko kaci Ubanka": Doguwa Yace kalamansa ba nufin zagi yake ba

Yana samun akalla Naira miliyan biyu duk wata amma yana kwatanta kansa da abokan zamansa.

Matashi
Wani Dalibin Da Yake Sai Da Biredi Ya Dan Kasuwa, Yana Samun Naira Miliyan 41.5 Duk Shekara Hoto: CNBC
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda Tunaninsa Ya Sauya

A cewar matashin Ellen, abin da ya dame shi shi ne ganin abokinsa na neman shiga jami’a.

Sai dai matashin mai yin burodin ya rungumi kaddara, yana mai cewa kowa yana da taasa qaddarar.

A cewar CNBC , bayan shekaru biyu, dalibin ya zama cikakken dan kasuwa kuma mai sana’ar Biredi. wanda yai qiayasin cewa yana samun sama da Naira miliyan 41 duk shekara.

A watan Maris na wannan shekara, ya fara bayyana a shirin Netflix's na gasar biredi.

Gasar wadda ke bawa masu yin biredi ko kek ƙirƙirar sura ta wani abu da biredin ko da kek din.

A ranar 18 ga Maris bidiyonsa ya zama cikin jerin bidiyo 10 da aka fi kallo a Amurka tsawon makonni hudu. An samu masu kallo da sharhi sama da mutum miliyan 100.

Kara karanta wannan

2023: Babu Wata Matsala Tsakani Na Da Atiku, Gwamna Wike Ya Faɗi Inda Matsalar Take a PDP

Ellen ya gaya wa CNBC cewa aiki tuƙuru da shawarwari masu hikima daga waɗanda suke ƙaunar ne su ka taimaka sosai.

Kafofin Sadarwa Na Zamani Sun Taimaka Sosai wajen Kasuwancinsa

Tun daga farko, Ellen ya ga alamun kafofin sadarwa na zamani suna da mahimmanci wajen habaka kasuwanci.

Amma ya ce kwazo da jajircewa sune jigonsa sannan yace uwa uba shafukan sada zumunta, sun taimaka

A cewarsa, tun farko baya jin dadi kuma abin ya bata masa rai.amma da jajirce ya ci gaba yanzu gashi kowa na sansa kuma na kallon bidiyona

Kafin kace mai sai gani da mabiya sama da 50,000 a Instagram kuma. sune jigon da ya sa nake samun dala $ 5,000 zuwa $ 9,000 a duk wata.

Wani Biloniya ya baiwa wata yar kasuwa mai shekaru 19 kyautar Naira miliyan 166 bunkasa kasuwancinta.

Legit.ng ta rawaito cewa wata ‘yar kasuwa mai suna Tania Speaks, mai shekaru 19 , ta samu karin jari daga mayukan da take siyarwa wan da adadin karin da ta samu ya tasar ma N166m

Kara karanta wannan

Magidanci Ya Yiwa Diyarsa Gwajin DNA a Boye, Ya Gano Ba Shine Ubanta Ba, Ya Mikawa Matar Sakamako a Bidiyo

Cewa matashiyar tace ta tattauna da 'ya'yan wanda ya taimaka mata mata guda biyu.

Attajirin ya ce zai zuba kudin ne a matsayin kaso 15 cikin 100 a kasuwancinta wanda ya birgeshi kuma yake so ‘ya’yansa mata su shiga sana'arta ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel