Mata 62 Ne Kadai Ke Zaman Gidan Yari Saboda Yanke Musu Hukuncin Kisa a Najeriya, Inji CGC

Mata 62 Ne Kadai Ke Zaman Gidan Yari Saboda Yanke Musu Hukuncin Kisa a Najeriya, Inji CGC

  • Shugaban hukumar gidan yari ya bayyana cewa, akwai akalla fursunoni 704,824 a gidajen yarin kasar nan
  • Hukumar ta bayyana cewa, akalla mata 62 ne ke kan hukuncin kisa a Najeriya, suna jiran a zartar a kansu
  • An ruwaito cewa, maza sun fi ba jami'an hukumar gidan gyaran hali ciwon kai a Najeriya, sabanin mata

FCT, Abuja - Shugaban hukumar gidan gyaran hali a Najeriya (NCoS), CGC Haliru Nababa ya ce, akwai mata da ke kan hukuncin kisa a gidajen yarin Najeriya akalla 62, sabanin 3,105 da ake dasu na jinsin maza, rahoton Vanguard.

Shugaban na hukumar NCoS ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis 15 ga watan Disamba ta bakin wakilinsa, DC Momoh Aliyu Salisu, wanda yace akwai fursunoni 74,824 a gidan gyaran halin kasar.

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar EFCC Ya Fadi Adadin Biliyoyin da Aka Samu Wajen Tsohon Akanta Janar

A cewarsa, fursunoni 50,955 maza ne da ke jiran hukunci, akwai kuma mata 1,223 da su ma suke jiran hukunci, Punch a baya ta kawo irin wannan rahoton.

Matan da ake dasu da ke kan hukuncin kisa a Najeriya 62 ne
Mata 62 Ne Kadai Ke Zaman Gidan Yari Saboda Yanke Musu Hukuncin Kisa a Najeriya, Inji CGC | Hoto: thecitypulsenews.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa, a yanzu haka akwai fursunoni maza 19,150 da mata 339 da aka yankewa hukunci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kirkiri shirye-shiryen habaka tarbiyyar fursunoni

Shi ma da yake magana, kakakin hukumar, AC Umar Abubakar ya ce, hukumar ta kirkiri shirye-shirye na musamman don tabbatar da koyawa fursunoni sana’o’in hannu da kuma daura su a turbar ilimi.

Ya bayyana cewa, a yanzu haka akwai ayyukan ci gaba 900 da hukumar ke tafiyarwa tsakanin fursunoni da jami’anta.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola a kwanakin baya ya yabawa matan Najeriya bisa rashin tsoma kansu cikin laifukan ta’addanci a kasar nan.

Ya kuma shawarce su da su ci gaba da nisantan ayyukan da ka iya jefa su cikin dana-sani da shiga gidan kaso.

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

Har ila yau, ya ce mafi yawan fursunonin da ke ba jami’in gidan gyaran hali ciwon kai maza ne ba mata ba.

An yanke wa dan Hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya

A makon nan ne aka yankewa wani dan jihar Kano kuma tsohon jami'in Hisbah da ya kashe wata bazawararsa saboda an hana shi ya aure ta.

An yankewa Dayyabu hukunci ne shekaru sama da 10 bayan da ya caccaka wa wannan bazawara tasa wuka.

Hujjoji sun kankama, an yanke masa hukunci, ba a san dai ko gwamnati za ta amince a kaddamar dashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.