Majalissar Dattijai Ta Umarci Babban Bankin Kasa yai Waiwaye Kan Tsarin Cire Kudi

Majalissar Dattijai Ta Umarci Babban Bankin Kasa yai Waiwaye Kan Tsarin Cire Kudi

  • A ranar talata majalissar ta shirya yin muhawara kan batun, sai dai muhawarar bata yiwuba sabida shugaban kwamitin majalissa kan banki baya nan
  • Tun da fari majalissar dattijai ta bukaci gwamnan babban bankin da ya bayyana a gaban ta dan amsa wasu tambayoyi kan tsarin da bankin ya fito da shi
  • Emefele, gwamnan babban bankin yace duk tsarin da ya fito dashi shugaba MuhammaduBuhari na sane da shi.

Abuja: Majalisar dattawa a ranar Larabar ta bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya yi duba kan batun tsarinsa na cire kudade. Rahotan Daily Trust

Karkashin sabon tsarin cire kudi babban bankin ya sanya yawan kudaden da mutane da kamfanoni za su rika cirewa duk mako daga N100,000 zuwa N500,000.

Hakan dai na zuwa ne bayan da majalisar dattijai ta yi la’akari da rahoton kwamitinta kan harkokin banki.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi watsi da karar dakatar da tsarin CBN na cire kudi

Dalilin hakan ta bukaci bankin da ya sake duba tsarin fitar da kudi, saboda yadda jama’a na korafi kan tsarin.

Sannan Majalissar ta umarci kwamitinta mai kula da bankuna kan ya duba yadda bankin zai duba tsarin da kuma sa ido kan yanayin aiwatar da tsarin.

Majalissar tace ta kuduri aniyar tallafa wa babban bankin a ci gaba da aiwatar da ayyukan samar da habaka tttalin arzikin kasa da bankin ya dau damara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed
Majalissar Dattijai Ta Umarci Babban Bankin Kasa yai Waiwaye Kan Tsarin Cire Kudi Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ran 15 Ga Watan Disamba Sabbin Kudi Zasu Fara Yawo a Tsakanin Yan Kasa

A wani labarin kuma yau sabbin kudin da babban bankin kasa ya sauyawa fasali zasu fara yawo a tsakanin yan kasa.

Farkon watan Nuwanban wannan shekarar babban bankin kasa CBN, ya fito da tsarin canjawa kudin Nigeria Fasali yana mai cewa hakan ne za sa tattalin arzikin Nigeria habaka da kuma dawo da kudin da ke hannun mutane sama da N2.6trn da suka kunshe a gidajensu.

Kara karanta wannan

Daga hannun PDP muka gaji matsalar Boko Haram : FG Ta Maidawa Atiku martani

Irinsu Dr. Yusuf Moda na ganin wannan tsarin ba abinda zai haifar sai tauyewa talakawa ko yan kasa yancinsu na hada-hada da kudade.

A wata zanatawa da yayi da jaridar Sahara Repoters, Legit.ng Hausa ta fassara, Dr. Moda yace babban bankin Nigeria ya shiga hurumin da ba nasa ba, kuma ya tauyewa yan kasa yancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida