Wiwi Nake Siyarwa don Samun na Bukatuna, Mai Kanjamau Ya Sanarwa Alkali
- Babbar kotun tarayya ta jihar Legas ta yankewa wata mata mai suna Bilkisu Lawal wacce ke ikirarin tana dauke da cutar kanjamau hukuncin shekara 1 a gidan yari
- Hakan ya biyo bayan kama wacce aka yankewa hukuncin tana harkallar safarar wiwi, inda NDLEA ta gurfanar da ita gaban kotu
- Sai dai, wacce aka gurfanar din ta tabbatar wa kotu tana dauke da cutar inda ta gabatar da takardar asibiti sannan da sana'ar take kula da kanta
Legas - Alkali Atokunle Faji ta babbar kotun tarayya ta Legas ta yankewa wata mata, Bilkisu Lawal wacce ke ikirarin tana da kanjamau hukuncin shekara daya a gidan yari.
Alkalin ta yanke hukuncin ne ga Bilkisu yayin sauraron shari'ar bayan an kamata da laifin safarar kilo biyar na wiwi, jaridar Punch ta rahoto.
Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi ce ta gurfanar da wacce aka yankewa hukuncin bisa zarginta da safarar wiwi.
Yayin gurfanarwan, mai gurfanarwa, Femi Adebayo ya sanar da kotu yadda aka kama ta dumu-dumu da wiwi a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2022 a gidanta na Odofin cikin Ebute Onijegi Iworo dake Badagry, jihar Legas.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda mai gurfanarwan ya bayyana, laifin ya ci karo da sashi na 11 sakin layi na 3 a kundun laifukan hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi ta Najeriya mai lamba 30, kuma abun horarwa ne karkashin wanan sashin.
Wacce aka yankewa hukuncin ta amsa laifin da ake tuhumarta
Bayan amsa laifin da ake tuhumarta dashi, mai gurfanarwan ya bukaci kotu da ta yanke mata hukunci daidai da yadda shari'a ta tanada.
Sai dai wacce aka yankewa hukuncin yayin neman sassauci ta sanar da kotu yadda take dauke da cutar kanjamau.
A cewarta, da sana'ar wiwi take kula da kanta, 'ya'yanta da mahaifiyarta da ta tsufa.
Da haka ne alkali ya bukaci ta gabatar da wata takardar asibiti don tabbatar da hakan, inda ta gabatar.
Alkaliya Faji, yayin hukuncinta a ranar Juma'a ta yankewa wacce aka kama da laifin hukuncin shekara daya a gidan yari, tare da cewa cutar da take fama da ita ba irin wacce gidan gyaran halin Najeriya zata kasa kula da shi bane.
Kotu ta umarci jami'an gidan gyaran halin Najeriya da su tabbatar sun ba wacce aka yankewa hukuncin kular da ta dace yayin da take tsare.
Asali: Legit.ng