Zagin Annabi: An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin da Kotu Zata Yanke Wa Sheikh Abduljabbar Hukunci
- Rahotanni daga Kano sun nuna cewa dakaru sun mamaye ko ina a kewayen fadar Sarkin Kano da safiyar Alhamis dinnan
- Kotun Shari'ar Musulunci mai zama a Kofar Nasarawa ta zabi yau a matsayin ranar yanke hukunci kan shari'ar Sheikh Abduljabbar
- Tun a watan Yuli na shekarar 2021, gwamnatin Kano ta gurfanar da Malamin a Kotu kan zargin maganganun ɓatanci ga Annabi SAW
Kano - Rahotanni da muke samu sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Anguwar Kofar Nasarawa kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami'an tsaro sun mamaye ko ina don tabbatar da igantaccen tsaro yayin da babbar Kotun Shari'a zata yanke hukunci kan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara yau.
Kotun Musulunci ta shirya yanke hukunci kan ƙarar da ake zargin Malamin da taba mutuncin fiyayyen halinta, Annabi Muhammad (SAW).
2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa
Wannan na zuwa ne watanni 15 bayan fara shari'ar Shehun Malamin a gaban Babbar Kotun Shari'ar Musuluncin mai zama a Kofar Kudu karkashin mai shari'a Ibrahim Sarki Yola.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sheikh Abduljabbar ya gurfana a gaban Kotun ne bisa tuhume-tuhumen da suka shafi wasu maganganun ɓata ƙima da darajar fiyayyen halitta manzon tsira, Annabi Muhammad SAW.
Ana zargin cewa irin kalaman da Shehin Malamin ke yi a wuraren karatuttuka ka iya tunzura jama'a kuma tsu hana zaman lafiya tsakanin mutane.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta maka Sheikh Abduljabbar a gaban Kotun tun a watan Yuli, 2021.
An girke jami'an tsaro kuma Abduljabbar ya isa Kotu
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa da safiyar Alhamis ɗin nan an girke dakarun tsaro ta ko ina a yankin kewayen Masarautar Sarkin Kano, wurin da Kotun ke zama.
Da misalin karfe 8:51 na safe, Malamin ya isa harabar dakin Kotun tare da rakiyar jami'an tsaron gidan gyaran Hali.
'Yan jarida, masu fafutukar kare hakkin ɗan Adam, lauyoyi da sauran masana shari'a duk sun samu wuri sun zauna suna dakon Alƙali ya shigo don fara zaman.
Na Yi Allah Wadai da Kisan Deborah, Ɗalibar da Ta Zagi Annabi a Sokoto, Atiku
A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya ƙara yin Allah wadai da kisan Deborah ɗalibar da ta zagi Annabi a Kwalejin Sakkwato
Watanni bayan faruwar lamarin, Atiku ya yi karin haske kan rubutun da ya sa aƙa goge a shafinsa na Allah wadai da kisan ɗalibar.
Yace tun lokacin ya umarci a Goge ne saboda ba da yawunsa aka wallafa ba, amma a cewarsa a rubutun da ya biyo baya, ya nuna rashin jin daɗinsa.
Asali: Legit.ng