"Shekaru Sun Ja" Wata Budurwa Ta Koka Kan Rashin Aure, Ta Nemi Wanda Zai Wuff Da Ita
- Wata mata da ta taba haihuwa ta bayyana takaicinta na rashin samun abokin rayuwa ga shekaru na ta ƙaruwa
- Matar yar kimanin shekaru 34 a duniya mai suna, Ayshatu Adams, tace zaman kaɗaici da rashin aure ya fara rikitata
- A cewarta mutane gudunta suke, duk wanda ya zo ba zai dawo ba saboda basu son ɗaukar nauyin ɗan da ba nasu ba
Wata matar mara aure wacce ta taɓa haihuwa sau ɗaya, Ayshatu Adams, ta jaraba sa'a ko za'a dace a kokarin neman wanda zai aure ta a Soshiyal midiya.
A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, Ayshatu, ɗalibar dake karantar aikin jinya a asibiti watau Nurse tace zata cika shekaru 35 a 2023 kuma har yanzun babu abokin rayuwa.
Ayshatu ta koka cewa duk saurayin da ya zo wurinta ba zai dawo ba saboda da yawansu basu son ɗaukar nauyin kula da ɗanta guda ɗaya.
Caudediyar matar ta bayyana cewa rashin auren nan ya fara ruɗa ta. Ta rubuta cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shekara mai zuwa zan cika shekaru 35 a duniya amma har yanzun bani da aure saboda kawai na taɓa haihuwa ina da ɗa."
"Duk mutumin da ya shigo rayuwata tun kafin magana tai nisa zai faɗa mun ba zai ɗauki nauyin kwan da ba shi ya saka ba."
Duba Bidiyon a nan
Mutane sun maida martani kan halin da take ciki
Abbati SK ya ce:
"Masoyiya duk wanda ya zo wurinki ya faɗa miki haka ba sonki yake da aure ba, abokin rayuwarki na gaske na nan zuwa kuma zai share miki hawaye."
Abubakari Rahinat ta ce:
"Mutumin da ya dace dake kuma mai tsoron Allah zai lalubo ki duk inda kika shiga, karki gaggawa a rayuwa. Allah na nan ya shirya miki kyauta ta musamman."
"Yara Sun San Komai" Dirarriyar Malama Ta Fallasa Wasikar da Dalibai Suka Aiko Mata, Mutane Sun Girgiza
Zee Money tace:
"Ki daina ɗaga hankalinki duk samarin da kike haɗuwa da su basu dace dake bane, Allah zai kawo miki mutum nagari."
Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Lambar Wani Mutumi a Gaban Matarsa, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Ja Hankali
A wani labarin an buga dirama mai kayatarwa a wani Bidiyo yayin da wata budurwa ta nemi lambar matashi a gaban matarsa
Kyakkyawar budurwar ta faɗa wa mutunin cewa ta gani kuma ta yaba don haka take neman lambar wayarsa, matarsa da suke tare abun ya bata mamaki.
Mutane sun maida martani kala daban-daban ganin yadda budurwar ta yi karfin hali duk da ganin yana tare da mai ɗakinsa.
Asali: Legit.ng