'Yan Ta’adda Sun Hallaka Mutane 4 a Wani Sabon Harin da Suka Kai a Kudancin Kaduna

'Yan Ta’adda Sun Hallaka Mutane 4 a Wani Sabon Harin da Suka Kai a Kudancin Kaduna

  • An sake samun mummunan yanayi a jihar Kaduna yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki kan mazauna Zangon Kataf
  • Akalla mutane hudu aka kashe, yayin da wasu suka jikkata da raunukan harbin bindiga daga 'yan ta'adda
  • Shugaban karamar hukuma ya bayyana abin d aya kamata kowa ya yi ganin ana dumfarar bukukuwan kirsimeti

Zangon Kataf, Kaduna - Kasa da sa’o’i 24 bayan da ‘yan ta’adda suka kashe mutum uku a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, an sake hallaka wasu hudu a wani sabon harin da tsageru suka kai kan mazauna karamar hukumar Zangon Kataf.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an kashe mutanen hudu ne a kauyen Kamuru da Unguwan Alulu a Zangon Kataf, yayin da aka kashe ukun farko a kauyukan Kpak da Malagum a ranar Talata da rana.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Halaka Abu Na-Iraqi da Abu-Na Masari, Gawurtattun 'Yan Ta'addan da Suka Addabi Katsina

Shugaban karamar hukumar Zangon Kataf, Hon. Francis Sani (Zimbo) ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an kashe mutum hudu, wasu hudu kuma sun samu raunuka.

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a Kaduna
'Yan Ta’adda Sun Hallaka Mutane 4 a Wani Sabon Harin da Suka Kai a Kudancin Kaduna | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewarsa, ya zuwa yanzu dai an dauke wadanda suka raunata zuwa asibiti saboda raunukan da suka samu daga harbin bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shawarin shugaban karamar hukumar ga jama'ar yankinsa

Shugaban ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankali kuma su yi hakuri su bar hukumomin tsaro su yi ayyukansu na dakile ‘yan ta’adda da ta’addanci a yankin, rahoton Daily Post.

A kalamansa:

“Ina kira ga al’ummar da abin ya shafa da sauran kauyukan makwabta da su sanya ido yayin da suke harkokinsu na yau da kullum.
“Muna dumfarar lokacin bikin kirsimeti. Dole mu dage da addu’o’i sannan mu kula domin zaunar da al’ummarmu lafiya."

Yayin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya ce yana kan wani aiki, ya kuma yi alkawarin ba da bayani ta hanyar da ta dace.

Kara karanta wannan

Borno: Mai Ciki Ta Rasa Ranta Bayan 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Mijinta

Zan kawo karshen rashin tsaro a Kaduna, inji Tinubu

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya ce zai tabbatar da kawo karshen 'yan bindiga da rashin tsaro a jihar Kaduna.

Bola Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar kamfen yankin Birnin Gwari na jihar a ranar Talata 12 ga watan Disamba.

Kananan hukumomi da yawa a Kaduna na fama da rashin tsaro, ana yawan samun hare-haren 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.