Wani Magidanci Na Cikin Tashin Hankali Yayin da Ya Dauko Karuwa Ya Kai Gidan Abokinsa, Ta Sace Kwal Din N6m

Wani Magidanci Na Cikin Tashin Hankali Yayin da Ya Dauko Karuwa Ya Kai Gidan Abokinsa, Ta Sace Kwal Din N6m

  • Wani magidanci ya shiga dana-sani yayin da ya dauko karuwa ya kawo gidan abokinsa, ta tsoma shi a cakwakiya
  • Wani mai amfani da shafin Twitter, Tunde Ososanya a rana Talata 13 ga watan Disamba ya yada labarin yadda karuwar ta sace zinare mai darajar N6m
  • Da yawan mutane a Twitter sun bayyana yadda suka ji da ganin abin da ya faru, akalla mutum 555 ne suka yi dangwale ga labarin

Wani ma’abocin Twitter y aba da labarin yadda karuwa ta tafka satar zinare mai darajar N6m na wani abokin mutumin da ya dauko ta ya kawo gidan abokinsa don aikata alfasha.

Tunde Ososanya ne ya yada labarin yadda lamarin ya faru, inda yace mutumin ya dauko ta ne domin su yi kwana daya ta yi tafiyarta.

Magidanci ya shiga rikici bayan da karuwarsa ta sace kwal din abokinsa ta fece
Wani Magidanci Na Cikin Tashin Hankali Yayin da Ya Dauko Karuwa Ya Kai Gidan Abokinsa, Ta Sace Kwal Din N6m | Hoto: LightFieldStudios/Getty Images (ba hoton asali bane wannan)
Asali: Getty Images

A cewar Tunde, mutumin ya dauko karuwar ne tare da kai ta gidan abokinsa, kamar yadda suka tsara a can ne za su yi abin da suke son aikatawa.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Buhari Ya Yi Magana Kan Gaskiyar Bacewar Naira Tiriliyan 89 a Bankuna

Karuwa ta tsoma shi cikin babbar matsala

Bayan kammala abin da suka zo yi, karuwar ta bar gidan, sai daga baya ne mutumin ya gano ta sirace da sarkar kwal mai darajar akalla Naira miliyan 6 na abokin nasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin an ce yana ma da aure, yanzu kuma ya shiga tashin hankali kamar yadda Tunde ya fada a shafin Twitter.

Yanzu dai abokin nasa ya kwace motarsa har sai ya nemo masa sarkar ko kuma ya biya shi kudaden da suka kai darajarta.

Labarin ya yadu a shafin Twitter sosai, mutane da dama sun yi ta martani a kai, a kasa mun tattaro muku abin da mutane ke cewa:

Martanin ‘yan Twitter

@Gee_day:

“Dama lalataccen mai aure ne. Haba malam, nawa ne kudin kama daki a otal?”

@Clayspink:

“Kadan daga abin da zai faru kenan ga mai taimakawa zina.”

Kara karanta wannan

Assha: Mata ta kama mijinta dumu-dumi ya karya azumi, abin da ya fada ya jawo cece-kuce

@FavouriteCoco:

“Ina dakunan otal. Hakan ya yi daidai da shi.”

@Priscy5_:

"Dan jin dadi kadan ya jawo maka rikici da wahalar watanni shida.”

@No_F4se:

“Kowane wasa na da wahalar hasashen sakamako, shin mai gidan ajiye sarkar Naira miliyan shida ya yi a fili?"

Mata ta kama mijinta yana lalata da kanwarta

A wani labarin kuma, wani mutum ne matarsa ta kama shi yana lalata kanwarta, uwa daya uba daya a cikin gidansa.

Matar ta shiga mamaki, ta tura kanwarta gida, ta gaza yi masa magana a aki, yanayin da ya jefa cikin matukar tsoro.

A gefe guda, ta fito kafar sada zumunta tana neman shawari, mutane da yawa sun tofa albarkacin bakinsu ga abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.