'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda 2 da aka Dade ana Nema a Katsina

'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda 2 da aka Dade ana Nema a Katsina

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina tayi nasarar sheke biyu daga cikin 'yan ta'addan da ake nema ido rufe a jihar Katsina
  • Hakan ya biyo bayan harin da suka kai Sokoto-Rima kwatas da burin yin garkuwa da wasu mazauna yankin
  • Ba tare da jinkiri ba, jami'an tsaron bisa jagoranci shugaban 'yan sandan yankin suka dakile harin bayan samun kiran neman agaji daga jama'a

Katsina - Rundunar 'yan sanda jihar Katsina tayi nasarar halaka wasu biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne kuma ana nemansu ido rufe, jaridar The Cable ta rahoto.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana yadda aka halaka su yayin da suka kai wani farmakin ba-zata kwatas din Sokoto- Rima na karamar hukumar Dutsin-ma dake jihar a ranar Talata 13 ga watan Disamban 2022.

'Yan sandan Katsina
'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda 2 da aka Dade ana Nema a Katsina. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Wasu gawurtattun 'yan ta'adda, Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari sun rasa rayukansu,"

Kara karanta wannan

Kaduna: Ana Tsammanin Halakar Shugaban 'Yan Bindiga Alhaji Lawan, Bayan Dakaru Sun Dira Maboyarsu

- cewar Gambo Isah, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, a wata takarda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A ranar 13 ga watan Disamba, 2022, misalin karfe 7:30 na dare, mun samu kiran neman agaji cewa 'yan ta'adda masu tarin yawa masu rike da bindiga kirar AK47 sun kai wa Sokoto-Rima kwatas na karamar hukumar Dutsin-ma hari, da burin yin garkuwa da wasu mazauna.
"Ba tare da jinkiri ba, kwamandan yankin da tawagarsa sun hanzarta zuwa yankin, wanda hakan yayi sanadin musayar wuta tsakaninsu da 'yan ta'addan, inda aka sheke gawurtattun 'yan ta'adda biyu dake jerin sunayen 'yan ta'addan da ake nema ido rufe."

- Takardar tace, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana yadda aka gano bindigu biyu kirar AK47 daga hannun 'yan ta'addan.

"Ana cigaba da sintiri don damko sauran 'yan ta'addan da suke tsere da raunukan harsasai,"

Kara karanta wannan

Borno: Mai Ciki Ta Rasa Ranta Bayan 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Mijinta

- Kamar yadda ya kara bayyana wa.

Sojin sama sun yi lugude kan sansanonin 'yan bindiga a Kaduna

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun yi ruwan wuta kan sansanonin 'yan bindiga dake kananan hukumomin jihar Kaduna.

Ana kyautata zaton sun sheke Alhaji Lawan, wani shugaban 'yan bindiga da suka yi wa ruwan wuta a gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel