Yanzu-Yanzu: Wata Kotu Ta Dakatar Da Batun Tisa Keyar Shugaban Yan Sandan Nigeria Zuwa Gidan Yari

Yanzu-Yanzu: Wata Kotu Ta Dakatar Da Batun Tisa Keyar Shugaban Yan Sandan Nigeria Zuwa Gidan Yari

  • A watan da ya gabata ne wata babban kotuntarayya mai zamanta a Abuja ta yanke hukucin tisa keyar shugaban yan sandan Nigeria gidan Dan-kande kan kin bin umarnin kotu
  • A wani martani da ya mayar mai magana da yawun rundunar yan sandan Nigeria, yace ko kadan ba'ayiwa shugaban yan sandan adalci ba sabida bai san ma da hukuncin ba balle ace yaki bi
  • An dai zargi shugaban rundunar yan sanda da laifin yiwa wani jami'inta ritayar dole alhalin lokacin ritayarsa baiyi ba

Abuja: Wata babban kotun tarayyar mai zamanta a Abuja, ta dakatar da hukunchin da aka yiwa shugaban yan sanda Nigeria na daurin wata uku a gidan 'dan kande

Mai shari’a Bolaji Olajuwon, a cikin hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, ya ce akwai shaidu a gaban kotun ta da ke nuna cewa shugaban yan sandan ya bi umarnin kotun.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Yan Sanda Sun Magantu Kan Gano Rubabbun Kudaden Da Aka Birne

Umarnin kotun farkon dai shine a maido da Patrick Okoli, wanda aka yi wa ritayar dole daga aikin ‘yan sanda.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa alkalin kotun da ya yanke hukuncin yayi la'akari da yadda shugaban yan sanda ya bi umarnin kotu, yana mai cewa:

“Saboda cikakken bin umarnin kotu da kuma tabbacin tabbatar da cikar umarnin, an ajiye umarnin, tare amsar rokon da shugaban yan sandan yayi ” injin kotun.

Mai shari’a Olajuwon, a hukuncin da ya yanke a ranar 29 ga watan Nuwamba, ya yanke wa IGP hukuncin daurin watanni uku a gidan yari, saboda ya ki bin hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a ranar 21 ga Oktoba, 2011, na mayar da wani dan sanda mai suna Okoli.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Okoli ya yi ritayar dole ne a shekarar 1992 a lokacin da ya ke aiki a rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi a matsayin babban Sufeton ‘yan sanda (CSP) ta hukumar ‘yan sanda (PSC a yanzu).

Kara karanta wannan

Daga hannun PDP muka gaji matsalar Boko Haram : FG Ta Maidawa Atiku martani

Wata Kotu A Abuja ta Tisa Keyar Shugaban Hukumar EFFCC Gidan Yari

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya abuja ta iza keyar shugaban hukumar EFCC gidan kaso sabida kin bin umarninta

Kotu dai ta umarci hukuma da ta maidawa wani mutum motarsa kirar "Range Rover", amma hukumar tai biris da umarnin kotun

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida