Majalissar Dattawa Zatai Muhawara Yau Kan Batun Tsarin Babban Bankin CBN Na Kayyade Cire Kudi
- A yau majalissar dattijan Nigeria zata kalkale maganar tsarin da babban bankin kasa CBN ya biniro da shi na cire kudi
- Daya daga cikin yan majalissar dattijan ne ya ja hankalin majalissar kan batun inda yace zai takura talakawan kasar nan musamman ma yan kasuwa
- Tun satin da ya gabata majalissar ta sanar da wannan satin a matsayin satin da zatai muhawa kan batun na CBN
Abuja: A jiya ne majalisar dattijai ta yanke shawarar yin muhawara kan tsarin kayyade kudaden da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi a kwanan baya a zaurenta.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana haka a zauren majalisar, biyo bayan wani kuduri da sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta Arewa, Olubunmi Adetunmbi ya gabatar.
Sai dai muhawara bata yiwuba, sabida shugaban kwamitin kula da bankuna na zauren majalissar dattijan bai samu damar halartar muhawarar ba, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan dai ya ja hankalin takwarorin sa kan rashin halartar shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin bankuna da inshora da sauran cibiyoyin kudi Uba Sani daga zauren majalisar.
Misis Ahmad, wacce ita ce mataimakiyar gwamnan babban bankin CBN kan tsarin daidaita harkokin kudi, ta bayyana wa kwamitin cikakkun bayanai game da tsare-tsaren bankin ranar Juma’ar da ta gabata bayan wani mitin da sukai da kwamitin.
An gabatar da cikakken bayanin da babban bankin na CBN ya bayar domin muhawara tare da tantance batun a zaman majalissar na jiya.
Sai dai Adetunmbi ya ce ba za a iya yin muhawarar ba saboda shugaban kwamitin wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, a jihar Kaduna, ya na jihar sa wajen gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na shiyyar Arewa maso Yamma.
Sanata Bulkachuwa ya ce kasancewar kwamitin bai gabatar da rahotonsa ba, bai kamata ya dakatar da muhawarar da majalisar dattawan ta shirya kan tsarin kayyade kudaden da babban bankin CBN ya fito da shi ba.
Ya ce:
“Bai kamata mu bar wannan abin ba tare da mu taba shi ba. Wannan lamari ne mai matukar muhimmanci, kuma ‘yan Najeriya na dakon abin da Majalisar Dattawa za ta yi, kamar yadda Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnan Babban Bankin ya dakatar da daukar mataki kan hakan. Ina kira ga Majalisar Dattawa da ta tattauna wannan batu a yau.”
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya dage kan dacewar a dage batun zuwa yau domin fara muhawarar.
Lawan ya ce:
“Ba na jin ace wai mun bar batun haka. ba ka fahimceni bane, baka fahimci sauran yan uwa a wannan zauren ba, a fahimtata, muna son samun cikakken goyan bayan kowa ne"
“Ina ganin ya dace a bai wa shugaban kwamitin dama ya zo ya gabatar da rahotonsa da kansa. Sanata Adetumbi mamba ne a kwamitin Banki.
Abun da Yan Nigeria ke Fata
Bukata dai da fatan yan kasa shine samar da yanayi mai kyau wanda bazai takura su ba, ko kuma wanda zai sa su ringa shan wahala wajen hada-hadar kudi.
Tsohon gwamnan babban bankin kasa, mallam Muhammadu Sunusi na boyu a wani fefn bidiyo yace wannan tsarin bazai takurawa talakawa ba.
Asali: Legit.ng