Wani Mutumi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ɗauki Ciki Bayan Wata 4 da Haihuwa

Wani Mutumi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ɗauki Ciki Bayan Wata 4 da Haihuwa

  • Wata mata ta wallafa bidiyon yadda Saurayinta ya murtuke bayan ta faɗa masa cewa ta samu juna biyu
  • Wannan ta faru ne watanni huɗu kacal bayan ta haifi kyakkyawar yarinya wacce aka hanga a cikin bidiyon
  • Mutane da dama sun maida martani kan Bidiyon yayin da wasu suka labarta abinda ya faru da su a soyayya

Wata Caudediyar budurwa ta ja hankali bayan Masoyinta ya sake ɗirka mata juna biyu watanni huɗu kacal bayan ta haifi yar kyakkywar yarinya.

A wani bidiyo da ta wallaha a dandalin TikTok, matar ta nuna yadda Saurayin na ta ya murtuke fuska bayan samun labarin ta ƙara ɗaukar juna biyu.

Juna biyu bayan wata 4 da haihuwa.
Wani Mutumi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ɗauki Ciki Bayan Wata 4 da Haihuwa Hoto: theperfectduo18/tiktok
Asali: UGC

Yayin da yake ɗauke da ɗiyarsu mai wata hudu a duniya a hannunsa, Mutumin ya yi hanzarin ɗago kai ya kalleta fuska a ɗaure. Ko kaɗan bai nuna farin ciki da jin haka ba.

Kara karanta wannan

Rawa Ko Hauka: Bidiyon Yadda Wani Sabon Ango Mai Zumuɗi Ya Rikito Kan Amarya Ana Tsaka da Rawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane sun maida martani a Soshiyal midiya

Malikabeyh ta rubuta cewa:

"Ya shiga ruɗani kai kace ba shi ne ya aikata ba har ta ɗauki cikin."

Reeslays ya ce:

"Ba shi kaɗai ba har yar ƙaramar ɗiyarsu da ke hannunsa ta yi takaicin jin haka, ina ta ya ku murna."

Alyassabryant96 ta ce:

"Watau ita kanta ƙaramar yarinyar labarin bai mata dafi ba ace ko shekara ɗaya ba ta yi ba amma har zata zama babbar yaya, lallai abu ya yi kyau."

@aaliyaharoha676 ta ƙara da cewa:

"Mako 8 kenan da ɗaukar nawa amma har yau abokin rayuwata bai ce ya yi farin ciki ba balle ya taya ni murna, na takaice muku zance ma ya bar ƙasar nan yanzu."

@samueltirado1 yace:

"Nima haka na murtuke fuska lokacin da aka haifa mun ɗiya mace sannan ɗana ya biyo baya. Duka duka tsakaninsu watanni 11."

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

Matar Aure Ta Kama Mijinta Na Rage Zafi Da Wata Yar Magajiya, Bidiyon Matakin da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane

A wani labarin kuma Wani magidanci ya gamu da bacin rana yayin da suka ci karo da matarsa yana shaƙatawa da wata budurwarsa

Matar ta sha mamakin yadda ta ga abokin rayuwarta da wata, ta fara zazzage masa buhun masifa a wani bidiyo da ya bayyana

Sai dai abun mamakin maimakon ya lallasheta sai aka ga yana kokarin kare budurwar daga cutarwan matarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262