Yanzu Yanzu: Jama’a Sun Tsere Yayin da Sojoji Suka Mamaye Wani Gari a Ebonyi, Sun Kona Gidaje
- Mazauna garin Obeagu da ke karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi sun tattara sun bar gidajensu
- Hakan na zuwa ne yayin da aka zargi sojojin Najeriya da kai mamaya garin a safiyar Litinin tare da kona wasu gidaje
- Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a gano ainahin dalilin da yasa sojojin suka kai mamaya garin ba
Ebonyi - Wani rahoto daga jaridar Punch ya nuna cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kai mamaya garin Obeagu da ke karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi.
Wasu shugabannin garin sun bayyana a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba, cewa dakarun sojin wadanda suka kai mamaya garin da misalin 5:00 na safe suna ta harbi kan mai uwa da wahabi sannan kuma sun yi zargin cewa sun kona wasu gidaje.
Ainahin abun da ya faru
Sahara Reporters ta rahoto cewa sojojin sun shigo garin da motocin Hilux 10 da tankunan yaki bakwai tare da jami'an sojoji sama da 100.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba a san ainahin dalilin da yasa sojoji suka kai mamaya garin ba, sai dai babu rahoto game da kishe wani zuwa yanzu. Wata mata daya kawai aka ce harbin bindiga ya sama.
Wasu yan bindiga sun farmaki Ebonyi
A halin da ake ciki, jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun farmaki Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, suna ta harbi kan mai uwa da wahabi lamarin da ya sa mazauna yankin neman tudun tsira.
Lamarin ya haifar da rudani a garin inda ya tilastawa yan kasuwa rufe shagunansu da komawa gidajensu.
Mazauna sun tsere
Wasu da dama sun samu mafaka a otel-otel da duk wuraren da suka samu don tsoron yin karo da yan bindigar.
Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya ce yan bindigar sun kona wani sashi na kasuwar Ahia Ofu da ke hanyar titin Abakaliki-Enugu.
Yan arewa ba za su sake zaban APC ba, Kungiya
A wani labari na daban, wata kungiya ta yan arewa ta bayyana cewa al'ummar yankin arewacin kasar ba za su sake yin APC ba a 2023 domin yin hakan tamkar halaka kai ne.
Kungiyar ta ce a iya saninta ba a taba samun yan gudun hijira a jihar Katsina ba sai a gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng