Gagarumar Gobara ta Tashi a Bene Mai Hawa 3 a Legas, An Tafka Asara
- Bene mai hawa uku dake Idumagbo Avenue a Obun-Eko dake Legas ya kama da gobara inda hankulan jama’a masu tarin yawa ya tashi
- Tuni masu kashe gobara da ceto suka garzaya don dakile wutar da ka iya laso bankin dake kasan benen da sauran masana’antu
- Gobarar ta kama wata ma’adanar kayayyaki ne da suka hada da tawul da zannuwan gado sun kone duk d aka rai daya bai salwanta ba
Legas - Wani gini mai hawa uku dake lamba 34 Idumagbo Avenue a Obun-Eko dake Legas a ranar Litinin ya kurmushe da wuta, jaridar Vanguard ta rahoto.
Gobarar ta fara wurin karfe 12:31 na rana daga hawa na uku na ginin inda abubuwa kamar tawul, zannuwan gado duk suka kone.
Sai dai babu wanda ya samu ko rauni daya.
Adeyeye Margaret, daraktan hukumar kashe gobar da ceto ta jihar Legas, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin tace masu kashe gobara daga Ebute Elefun da Oniru ne suka je wurin don kashe wutar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Wutar da aka gane tana ci wurin karfe 12:31 na rana ta samu jami’ai daga tashoshin Ebute Elefun da Oniru wadanda suka je kashe gobarar.
“Wutar ta kama wata ma’adanar kayayyaki dake hawa na uku dake dankare da kaya kamarsu tawul, zannuwan gadaje da sauransu tare da wani bankin ‘yan kasuwa a kasa.
“Masu kashe gobara tare da hukumomin da lamarin ya shafa sun yi nasarar kashe gobarar yayin da suka kubutar da bankin da sauran gine-ginen dake kasa.
“Har a halin yanzu babu wanda ya samu rauni ko ram da aka rasa yayin da ake cigaba da bincike kan musabbabin gobarar.”
Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne
Gobara ta kama fitacciyar kasuwar Onitsha
A wani labari na daban, ‘yan kasuwa a babbar fitacciyar kasuwa Onitsha ta jihar Anambra sun koka kan asarar da suka tafka.
Hakan ya biyo bayan gobarar cikin dare da ta tashi tare da lamushe musu kayayyaki masu tarin yawa.
Gobarar da ta fara cikin dare ta cigaba da zuwa safiya da tasowar hantsi duk da kuwa jami’ai sun dinga kokarin ganin su kashe ta.
Ta tashi a Kano Street dake cikin kasuwar.
Asali: Legit.ng