Attajirin Nan Na Kano, AA Rano ya 'Bare Jirgin N4.2bn A Leda Dan Fara Jigilar 'Yan Kasa
- Bayan samun amincewar gwamnatin tarayya, nan ba da jimawa ba Rano Air zai fara shawagi a sararin samaniyar Nigeria
- Kamfanin jirgin mallakin hamshakin dan kasuwa mai hada-hadar mai, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano
- Don fara aikin kamfanin jirgin, Rano ya kashe sama da Naira biliyan 4.2 wajen siyan sabbin jiragen
Kano: Kamfanin jiragen sama na Rano Air a Najeriya ya samu cikakkiyar amincewar fara aiki daga gwamnatin tarayyar Nigeria.
Kamfanin ya nemi lasisin sufurin jiragen sama (ATL) tare da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nigeria (NCAA) a cikin watan Janairu don gudanar da ayyukan jigilar fasinja da kayayyaki kamar yadda aka tsara a ciki da wajen Najeriya.
Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai da sadarwa na zamani, ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba, 2022, cewa an samu cikakken ikon fara yi.
Ya kuma bayyana cewa yanzu haka an shirya yadda kamfanin zai fara jigilar fasinjoji a fadin kasar nan.
Ya rubuta:
"Rano Air, daya daga cikin sabbin kamfanonin jiragen sama na Najeriya, wanda aka kafa a shekarar 2019, ya samu amincewar Gwamnatin Tarayya don gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na gida a garuruwan Legas, Kano, Abuja, Kaduna, Sokoto, Gombe, Yola, Maiduguri, da Asaba."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin Rano Air
Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, Shugaban Kamfanin AA Rano kuma dan asalin Kano , shine mamallakin Rano Air.
Shigowar Rano a harkar sufurin jiragen sama zai daga tare habaka tattalin arzikin Najeriya.
A shirye-shiryen gudanar da aikin Rano Air, Dailytrust ta ruwaito cewa ya samu jirage wanda suke da lamabar EMB-145LRs guda hudu don fara aiki awannan shekarar.
Manufofin Babban Bankin Kasa Akan Fitar Da Kudi Tauyewa 'Yan Nigeria Hakk'ine – Masanin Kudi, Muda Yusuf
Binciken da Legit.ng ta yi ya nuna matsakaicin farashin Embraer ERJ-145LR da ake sayarwa a GlobalAir.com ya kai dalar Amurka $2,395,000 (N1.09 biliyan).
Haka kuma Rano ya samu nasarar karbar lasisin zirga-zirgar jiragen sama (ATL) daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).
Ana sa ran kamfanonin jiragen saman nasa zasu ringa jigilarfasinjoji da kaya daga jihohin Legas, Kano, Abuja, Kaduna, Sokoto, Gombe, Yola, Maiduguri da Asaba.
Tarihin Rano
An haifi Alhaji Auwalu Abdullahi Rano wanda aka fi sani da A. A Rano a ranar 9 ga watan Yuni 1944 wanda ya fito daga yankin Hausa-Fulani da ake kira Lausu a karamar hukumar Rano a Jihar Kano Najeriya.
Ya samu kudinsa ne daga bunburutun man fetur wanda ya fara a tun a shekara ta 1994.
wani rahoton ya nuna cewa ya gina kantunan sa na farko a jihar Kano a shekarar 1996, sannan ya kafa kamfanin A. A Rano Nigeria Limited a shekarar 2002.
Dangote ya bayyana shirin daukar matasan Najeriya 300,00 aiki
A wani labarin kuma , Dangote zai fara daukar ‘yan Najeriya 300,00 aiki a wani gagarumin shirin aikin yi da yake so ya fara.
An kaddamar da wani sabon shafi na daukar aikin yi ga ‘yan Najeriya a matatun mai da sukari da 'dangote ke shirin budewa.
Aikin a matatar ta da ke Legas ya hada da wurin kwana kyauta ga ma’aikata.
Asali: Legit.ng