Matar Aure Ta Yi Bidiyon Mijinta Yana Tikar Wankin Kayanta, Jama’a Sun Yi Martani

Matar Aure Ta Yi Bidiyon Mijinta Yana Tikar Wankin Kayanta, Jama’a Sun Yi Martani

  • Wata matashiya yar Najeriya wacce ke cike da farin ciki kan yadda mijinta ke taimaka mata da aikin gida ta haddasa cece-kuce a yanar gizo
  • Matar ta ci gaba da jinjinawa mijin nata yayin da yake wankin kayanta cike da kulawa, yana daukarsu daya bayan daya
  • Mata da suka yi tururuwa a sashin sharhinta suma sun magantu kan yadda abokan zamansu ke ririta su a gida

Wata matashiyar mata yar Najeriya mai suna @geeneeposh, ta haddasa cece-kuce a TikTok bayan ta wallafa wani dan gajeren bidiyo da ke nuna mijinta yana wankin kayanta.

Bidiyon ya nuno mijin a baya yana aikin wanki, matar ta jinjina masa tana mai cewa lallai shi din gwarzo ne a cikin maza.

Mata da miji
Matar Aure Ta Yi Bidiyon Mijinta Yana Tikar Wankin Kayanta, Jama’a Sun Yi Martani Hoto: TikTok/@geeneeposh
Asali: UGC

Miji na wanke kayan matarsa masu datti

Matar ta jinjinawa maza masu tallafawa matansu da aikin gida. Yayin da matar ke bidiyon na TikTok, mijin ya ci gaba da wankinsa.

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Garzayo Najeriya Daga Turai Domin Haduwa Da Sahibinta, Bidiyonsu Ya Yadu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matan aure sun je sashin sharhi don yin magana game da sa'an miji da tayi yayin da wasu suka bayyana yadda gidan aurensu yake.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

princessigben ta ce:

"Allah ya albarkaci mijinki babu irinsa yanzu girman kai ya kashe sauran."

Gifty ta ce:

"Har yanzu mahaifina na wanke kayan maamata, ban taba ganin mahaifiyata tana wanke kayanta ba, abun da mahaifina yafi kauna shine wanki."

Agumba Loveth ta ce:

"Nawa baya wanki amma ya saukaka mun ta hanyar siya mun injin wanki."

Naturallyziny ta ce:

"Mijina yana mun wanki. Odogwu da kansa."

Ta yi martani:

"Kwarai faa! Basu da yawa shiyasa mutane da dama basu gane ba."

Dattijuwa mazauniyar Turai ta biyo saurayinta Najeriya

A wani labarin, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan ganin bidiyon wata dattijuwar mata da ta biyo habibinta Najeriya tun daga Turai domin su soye.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Matar Aure Ta Saki Bidiyon Mijinta Yana Musu Girki Cikin Nishaɗi A Gida, Tace Ba Za Ta Koka Ba

Matar ta cika da farin ciki yayin da ta dauki bidiyon isowarta kasar har zuwa yadda saurayin nata ya sauketa da gyaran gashi da aka mata.

Lamarin ya baiwa mutane a soshiyal midiya mamaki yayin da wasu da dama suka shawarce ta a kan ta yi aiki da lura kafin ya yi mata ta yan maza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng