Dirarriyar Budurwa Mai Tsoron Ubangiji Ta Bayyana Yadda ‘Samarin Shaho’ ke Gudunta

Dirarriyar Budurwa Mai Tsoron Ubangiji Ta Bayyana Yadda ‘Samarin Shaho’ ke Gudunta

  • Wata matashiyar kyakyawar budurwa ta bayyana cewa mazan dake son jikinta suna gudunta bayan sun gano inda ta dosa
  • Budurwar tace akwai abubuwa masu tarin yawa da ba zata lamunta ba kuma duk wata alaka da ba ta Allah da Annabi ba bata so
  • Jama’a masu tarin yawa sun cika sashen tsokacin wallafar da tayi inda suka dinga yabawa natsuwarta tare da fatan alheri

Wata budurwa mai amfani da suna @rebeccalukika a shafinta na TikTok wacce a koda yaushe take batun bautar Ubangiji ta je dandalin sada zumuntar zamani ta sanar da jama’a abinda ba zata lamunta ba yayin alaka.

Budurwa mai tsoron Allah
Dirarriyar Budurwa Mai Tsoron Ubangiji Ta Bayyana Yadda ‘Samarin Shaho’ ke Gudunta. Hoto daga TikTok/@rebeccalukika
Asali: UGC

Budurwar a bidiyon ta bayyana cewa mazan da suke nuna suna son ta kwatsam suke gane cewa ita mai bautar ubangiji ce.

Ubangiji ne a gabana, Budurwa tace

Kara karanta wannan

"Mun Rantse" Wata Budurwa Ta Kaiwa Saurayinta Da Ya Haukace Abinci, Bidiyon Yadda Ta Nuna Masa So Ya Ja Hankali

A wani wuri a bidiyonta, an gan ta a mumbarin coci tana da’awa kan Ubangiji. Budurwar ta kara da cewa ba zata iya kwanciya da kowanne namiji ba kafin aure.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamanta:

“Ba zan lamunci wani abu ba da ya wuce alakar da aka gina kan turbar Yesu, wacce Ubangiji ake sakawa a gaba.”

Kalla bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

A lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya samu tsokaci sama da 1,000 yayin da ya samu jinjina sama da 60,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin.

Sidney Deane yace:

“Abinda kawai nake gani a nan shi ne nasara bayan nasara.”

Paul Bowen yace:

“Babu abinda ya kasance ba daidai ba a wannan, abinda kawai zan ce shi ne ki bi a sannu yadda ki ke yi kuma ki tabbatar a koda yaushe don Ubangiji ki ke yi.”

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Babban Abin da Yake Sa Jami'ai Tafka Sata a Gwamnati

Bertilla.a yace:

“Wannan shi ne hakikanin gaskiya.”

Positivity100 yace:

“Haka nake son in yi rayuwata. Ina fatan Ubangiji ya bani juriya kuma zan yi.”

Dessie tace:

“Ina ta gano irin mutane na, Nagode mahalicci.”

Bly yace:

“Je ki gimbiya, cigaba da yin nasara.”

Andrew Walters yace:

“Wannan ba komai bane face abinda zai bude miki kasuwa.”

Josephine Bonsu363 tace:

“Gaba dai gaba dai gimbiya ke ce duk abinda ake bukata.”

Kojo Kuda West yace:

“Ba zan iya jira har sai nayi aure ba.”

Praisesmike yace:

“Ta yaya ki ke tsara rayuwarki da addinin Kiristanci?”

’Yar gwagwarmayar neman yancin mata na neman miji

A wani labari na daban, wata budurwa dake don a daidaita ‘yancin mata da maza ta koka kan rashin miji.

‘Yar gwagwarmaray tace ta janye wannan ra’ayin nata kuma zata zage damtse wurin yi wa duk namijin da zai aureta biyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng