Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Buhari Gidan Gyara Hali Saboda Aikata Zamba
- Jam'iyyar APC mai mulki ta maka Uche Ogah a kotu bisa zarginsa da kirkirar takardar zaben fidda dan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar Abia
- Mai shari Ngozi N. Nwangwa ta kotun majistare da ke zama a Umuahia ta yi umurnin garkame tsohon ministan ma'adinai a magarkama
- Kotun ta yi umurnin kama Ogah a duk inda aka gan shi sannan a tsare shi a gidan gyara hali mafi kusa
Wata kotun Majistare da ke zama a Umuahia ta tura tsohon karamin ministan ma'adinai da karafa, Dr. Ucge Ogah, gidan gyara hali a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba.
Yayin da take zartar da hukuncinta, kotun ta yi umurnin kama Ogah da kai shi gidan gyara hali mafi kusa a jihar Abia, jaridar Punch ta rahoto.
Jam'iyyar All Progressives Congress ta shigar da kara a kan Ogah tana mai zargin cewa tsohon ministan bai shiga zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jam'iyyar ba wanda ya gudana a ranar 26 ga watan Mayu.'
Zunubin da Uche Ogah ya aikata
APC a kararta mai lamba No. UMSC/362/2022 ta kuma bayyana cewa duk da cewar Ogah bai shiga zaben fidda gwanin ba, ya yi gaban kansa wajen kirkirar takardar sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jam'iyyar mai mulki, Ogah ya aikata hakan ne da nufin cewa ana iya aiki da shi a matsayin na hakika.
A shari'ar, mai karar ta bayyana cewa abun da Ogah ya aikata ya sabawa jam'iyyar da sahihin dan takararta na gwamna a jihar Abia, Cif Ikechi Emenike.
Mai kara ya ce Ogah ya aikata laifin da ya ci karo da sahi 465 na dokar laifi a Abia kuma hukuncinsa na karkashin sashi 467.
A hukuncinta, Ngozi N. Nwangwa, mai shari'ar da ke jagorantar karar, ta riki cewa wanda ake karar ya aikata laifin da aka tuhume shi.
"Na yarda cewa wanda ake karar bai da kariya.
"Don haka na hukunta Dr Uche Ogah kan laifin kamar yadda aka tuhume shi."
Ta kuma umurci hukumomin tsaron da abun ya shafa da su kama Ogah a duk inda suka gan shi sannan su ajiye shi a magarkama mafi kusa, rahoton Thisday.
Mai shari'ar ta kara da cewar da wannan hukunci nata, ana sa ran tsohon ministan ya ci gaba da kasancewa a magarkama har zuwa ranar da za a gurfanar da shi gaban kotu don yanke hukuncin karshe.
Wahalar fetur: DSS ta gargadi dilallan man fetur da kamfanin NNPC
A wani labarin kuma, hukumar DSS ta yi gargadin yin kamen masu hannu a lamarin da ya kai ga ci gaba da yin layi a gidajen mai a kasar nan bayan sa'o'i 48.
Rundunar tsaron ta yi wannan gargadi a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba yayin da ake fama da wahalar mai a fadin kasar.
Asali: Legit.ng